Home Back

NLC ta Koro Dalibai da Abokan Huldar Bankuna Saboda Yajin Aiki a Kaduna

legit.ng 2024/7/7
  • Kungiyar kwadago ta NLC a jihar Kaduna ta tilastwa makarantu, bankuna, da asibitoci da ma rufe wasu ma'aikatun yayi da aka fara yajin aiki a yau Litinin
  • Rahotanni sun bayyana cewa tun da sanyin safiyar Litinin, kamar da misalin karfe 7.00 na safiya ne mambobin NLC suka shiga makarantar fasaha ta jihar
  • Sun koro daliban da suka riga suka shiga ajujuwa, yayin da dalibai suka fara bayyana damuwa kan halin da karatunsu zai iya shiga saboda yajin aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna- Yayin da kungiyar kwadago ta shiga yajin aikin gama gari a wannan Litinin din, mambobinta sun tilastawa makaranta da ma’aikatu bin dokar rufe wuraren aiki a jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa mambobin NLC sun koro daliban makarantar fasaha ta Kaduna daga ajujuwansu dazun nan.

Kaduna
Yajin Aiki: NLC ta tilasta bin umarnin shiga yajin aiki a Kaduna Hoto: NLC HQ/Senator Uba Sani Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa da sanyin safiya, misalin karfe 7:00, 'yan kungiyar suka shiga filin makarantar na Unguwar Rimi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga daliban makarantar sun shiga takaicin yadda yajin aikin zai shafi karatunsu, domin a halin da ake ciki ba a san ranar janye yajin aikin ba.

NLC ta rufe asibitoci, bankuna a yajin-aiki

Rahotanni daga jihar Kaduna sun tabbatar da yadda 'yan kungiyar kwadago na NLC suka rufe wasu muhimman wurare a jihar yayin da aka fara yajin aikin sai baba ta gani, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Shugabannin NLC sun rufe cibiyar kula da lafiya kunne ta kasa, tare da korar ma’aikatan dake ciki, har ma da hana marasa lafiya shiga.

Haka kuma ‘ya’yan kungiyar sun kori masu hulda da bankuna yayin da suka shiga bankunan domin a duba matsalolinsu daban-daban.

A tattaunawarsa da manema labarai, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) a jihar, Abdullahi Danfulani ya bayyana cewa kowa ya bi yajin aikin.

Shugaban majalisa ya fadi illar bukatar NLC

A baya mun kawo muku labarin cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ce kuɗin da kungiyar NLC ta nema a matsayin mafi karancin albashi zai yi illa ga ma'aikata.

Ya ce kamfanoni masu zaman kansu ba za su iya biyan albashin ba, wanda dole daga bisani su fara korar ma'aikata, kuma hakan zai janyo matsalar rashin aikin yi.

Asali: Legit.ng

People are also reading