Home Back

Dalilan cire wa Nijar, Mali da Burkina Faso takunkumi – ECOWAS

premiumtimesng.com 2024/4/28
RA’AYIN PREMIUM TIMES: ECOWAS da matsalolin da suka dabaibaye yankin Sahel

Kungiyar Bunƙasa Ƙasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, wato CDEAO da harshen Faranshi, ta bayyana cewa ta cire wa Nijar, Mali da Burkina Faso takunkumi ne saboda a samu dunƙulewar haɗin kai da wanzar da tsaro a yankin.

Shugaban ECOWAS Omar Touray ne ya bayyana haka bayan ganawar da shugabannin ƙasashen ECOWAS suka yi ranar Asabar a Abuja.

Ya ce ECOWAS ta dubi yanayin da ake ciki a yanzu, tare kuma da dubi da gabatowar watan Ramadan, sai kuma yadda takunkumin ya jefa mutane da yawa cikin mawuyacin hali.

Ya ƙara da cewa an kuma yi duba da irin kiraye-kirayen da wasu mashahuran mutane suka riƙa yi, ciki kuwa har da tsohon Shugaban Najeriya na Mulkin Soja, Yakubu Gowon, wanda ya na cikin waɗanda suka kafa ECOWAS cikin 1975.

Cikin makon jiya ne dai Gowon ya je Fadar Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya ce a cire wa Nijar, Mali da Burkina Faso takunkumi, kuma ya roƙi su janye ficewa daga ECOWAS.

Tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin Soja, kuma ɗaya daga cikin shugabannin da suka kafa ECOWAS cikin 1975, ya yi kira ga ƙungiyar ta ƙasashen Afrika ta Yamma cewa ta cire takunkumin da ta ƙaƙaba wa ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.

Ya ce “Dukkan shugabannin ƙasashen Afrika ta Yamma su maida hankali wajen gaggauta cire da ƙasashen uku takunkumi.”

Gowon da ya na cikin shugabannin da suka kafa ECOWAS cikin 1975, lokacin ya na shugaba na mulkin soja.

Ya nuna damuwar sa dangane da abubuwan da ke ta faruwa a cikin ƙasashen ƙungiyar ta ECOWAS.

Ya bayyana hakan cikin wata wasiƙa da ya aika wa dukkan Shugabannin Ƙasashen ECOWAS.

Ya rubuta wasiƙar dai a ranar 13 ga Fabrairu, kamar yadda PREMIUM TIMES ta ci karo da ita a ranar Laraba ɗin nan.

Ya rubuta wasiƙar mako ɗaya bayan Mali, Nijar da Burkina Faso sun ayyana ficewar su daga ECOWAS, su na yi wa ƙungiyar zargin cewa ta tashi daga kare muradun ƙasashen Afrika ta Yamma, ta zama ‘yar amshi Shatan Turawan Yamma, musamman ma ƙasar Faransa.

An dai ƙaƙaba wa ƙasashen uku takunkumi ne bayan sun kifar da gwamnatin farar hular ƙasashen.

Giwon ya ce abin ya na baƙanta masa rai ganin yadda rashin haɗin kai tsakanin ƙasashe ke neman kekketa rigar mutuncin ECOWAS, bayan ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso daga ECOWAS.

Ya ce rashin haɗin kai tsakanin ƙasashen ECOWAS da kuma takunkumi zai illata talakawa ne kaɗai, waɗanda an kafa ƙungiyar ce domin amfanin haɗin kai da zamantakewa tsakanin su.

Gowon ya kuma roƙi ƙasashen uku da suka fice da su koma cikin ƙungiyar. Kuma ya yi kira da a gaggauta taron ECOWAS kan batun matsalar tsaro, zaman lafiya da arzikin yankin da kuma rawar da ƙasashen Turai ke takawa a yankin.

Dangane da cire takunkumi da aka yi kwanaki uku bayan kiran da Gowon ya yi, ECOWAS ta ce, “ficewar Mali, Nijar da Burkina Faso daga ECOWAS zai shafi siyasa, zamantakewa, tattalin arziki na ƙasashen uku da na sauran ƙasashen ECOWAS.

“Ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun amfana da tallafin yaƙi da Boko Haram da sauran laifuka har na Dala miliyan 100 daga UMR, ta hanyar ƙoƙarin ECOWAS.

Haka kuma anyi la’akari da cewa ficewar ƙasashen uku zai shafi hulɗar su da sauran ƙasashen ECOWAS, domin hakan zai sa tilas ‘yan ƙasashen ba za su shiga wata ƙasa ba sai da biza.

 
People are also reading