Home Back

Bola Tinubu Zai Gana da Gwamnoni, Za Su Tattauna Kan Mafi Karancin Albashi a Villa

legit.ng 6 days ago
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi za su tattauna batun mafi ƙarancin albashi a taron NEC ranar Alhamis
  • Tun farko dai majalisar zartaswa ta tarayya ta ɗage batun ƙarin albashin a zaman da ta yi ranar Talata, 25 ga watan Yuni
  • Femi Gbajabiamila ya ce duk da ba a saba gani ba, Tinubu zai halarci taron majalisar ƙoli ta tattalin arzki (NEC) yau Alhamis, 27 ga watan Yuni, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron majalisar tattalin arziki ta tarayya (NEC) yau Alhamis a fadar gwamnati da ke Abuja.

Ana sa ran a wannan taro Bola Tinubu da gwamnonin jihohin Najeriya za su tattauna batun sabon mafi ƙarancin albashi da ake ta kace-nace.

Bola Tinubu da shugabannin kwadago.
Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron NEC a fadar shugaban kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nigeria Labour Congress HQ Asali: Facebook

Kamar yadda This Day ta ruwaiti, wannan taro na zuwa ne kwanaki 3 bayan majalisar zartaswa (FEC) ta ɗage batun mafi karancin albashi a zamanta na ranar Talata.

Majalisar ta bayyana cewa ba za ta yi gaban kanta ta yanke hukunci ba, ta bai wa Bola Tinubu damar ya ƙara tuntuɓar waɗanda abun ya shafa don cimma matsaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta ruwaito cewa waɗanda Tinubu zai tuntuɓa kafin yanke hukunci sun haɗa da gwamnoni, kananan hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu.

Femi Gbajabiamila ya faɗi inda aka kwana

Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila ya tabbatatda cewa Shugaba Tinubu zai halarci taron NEC da aka shirya yau Alhamis, 27 ga watan Yuni.

Gbajabiamila ya faɗi haka ne yayin da ya jagoranci manyan jami'an gwamnati suka je ta'aziyyar rasuwar surukar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

Ya ce:

"Zai halarci taron gobe (Alhamis, 27 ga watan Yuni, 2024) shiyasa zamansa a Abuja ke da matuƙar muhimmanci.
"Zai shiga taron NEC wanda da wuya idan ya taba halarta, ina tunanin wannan ne karo na farko."

Gwamnaoni 36 sun gana kan ƙarin albashi

A wani rahoton kuma Gwamnoni 36 na Najeriya sun tabbatar da cewa ma'aikata za su samu ƙarin albashi mai tsoka a tattaunawar da ake yi.

AbdulRahman AbdulRasaq na jihar Kwara ne ya bayyana haka bayan taron ƙungiyar gwamnoni wanda ya gudana ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

People are also reading