Home Back

Kotu Ta Yi Hukunci Kan Rigimar Masarautar Kano, Aminu Bayero Zai Bar Fadar Nasarawa

legit.ng 2024/9/27
  • A yayin da rigimar masarautar Kano ta kasa lafawa, kotu ta dakatar da Aminu Ado Bayero daga gabatar da kansa a matsayin sarki
  • An ruwaito cewa kotun ta kuma umarci ‘yan sanda da su kori Aminu Bayero daga gidan sarautar Nassarawa inda ya ke zaman fada
  • Wannan dai na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya ta ba gwamnatin Kano umarnin dakatar da aiwatar da dokar rusa masarautu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Rahotan da muke samu yanzu na nuni da cewa wata kotu ta dakatar da tsige sarki Aminu Ado Bayero daga gabatar da kansa a matsayin sarki.

Haka zalika an ruwaito cewa kotun ta kuma umarci ‘yan sanda da su kori Aminu Bayero daga gidan sarautar Nassarawa.

Kotu ta yi magana kan rigimar masarautar Kano
Kotu ta hana Aminu Bayero gabatar da kansa a matsayin sarkin Kano. Asali: Facebook

An tabbatar da hakan ne a wani sako da shahararren dan jarida kuma mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya fitar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta dakatar da nada sarkin Kano

Wannan ya biyo bayan umarnin da wata babbar kotun tarayya ta bayar na dakatar da gwamnatin jihar daga rusa masarautun da tsohon gwamna Abdullahi Ganduja ya kirkiro.

Kotun ta kuma dakatar da Abba Yusuf daga nada wani sabon sarki a Kano har sai ta yanke hukuncin karshe kan karar da aka shigar gabanta.

Mai shari’a Mohammed Liman ya bayar da wannan umarni ne a cikin karar da Sarkin Dawaki Babba na masarautar Kano, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar.

An ba sarakunan umarnin barin fada

Idan dai za a iya tunawa, Gwamna Abba Yusuf ya amince da dokar Masarautar Kano da majalisar dokokin jihar ta yi wa kwaskwarima tare da sanar da maido da Sanusi II a matsayin sabon sarki.

Sabuwar dokar ta soke dokar shekarar 2019 da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya sanya wa hannu wadda ta kafa masarautu biyar a jihar.

Gwamnan jihar ya kuma umarci sarakunan da aka tsige da su fice daga gidajen sarautar cikin sa’o’i 48 tare da mayar da kadarorin gwamnati da ke hannun su.

Aminu Bayero ya koma fadar Nasarawa

Sai dai yayin da wasu sarakunan suka yi biyayya, Aminu Ado Bayero ya ki amincewa da umarnin, inda ya dogara da cewa kotu ta dakatar da batun tsige shi.

Lamarin dai ya haifar da zanga-zanga a ranar Lahadi inda aka ga magoya bayan Aminu Bayero suna neman gwamnati ta bi umarnin kotu.

Ko a yau Litinin, mun ruwaito cewa Aminu Ado Bayero ya yi zama a fadar Nassarawa yayin da Muhammadu Sanusi ya gudanar da na sa zaman a fadar Kano.

An gudanar da Sallar Al-Qunut a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa magoya bayan sarakunan da gwamnatin Kano ta sauke daga mulki sun gudanar da gangamin taron addu'o'i da Sallar Al-Qunut a Kano.

An ruwaito cewa an gudanar da sallar tare da yin addu'o'i a kusan dukkanin masarautun da abin ya shafa da fatan maido da sarakunan.

Asali: Legit.ng

People are also reading