Home Back

Ranar Yara: Tinubu Ya Yi Alkawura Kan Inganta Rayuwar Kananan Yara

legit.ng 2024/6/18
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya yaran Najeriya murna kan bikin ranar yara ta duniya a yau Litinin, 27 ga watan Mayu
  • Shugaban kasar ya ce lallai gwamnatinsa za ta cigaba da ƙoƙarin inganta rayuwar manyan gobe domin tabbatar da cigaban Najeriya
  • Bola Tinubu ya bayyana haka ne a cikin wani sako da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Ajuri Ngelale ya wallafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya yaran Najeriya murnar zagayowar ranar yara ta duniya.

Tinubu
Bola Tinubu ya yi alkawarin inganta ilimin yara. Hoto: Ajuri Ngelale Asali: Facebook

Bola Tinubu ya taya yara murna ne cikin sakon da mai taimaka masa kan harkar sadarwa, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Shugaban kasar ya bayyana cewa yara sune tushen cigaba a kowace al'umma saboda haka ba zai yi wasa da lamarin su ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi alkawari ga yara

A cikin sakon, Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce zai tabbatar da inganta rayuwar yara a Najeriya musamman a harkar ilimi.

Ya ce za a samar da yanayin mai aminci da yaran Najeriya za su cigaba da koyon karatu tare da inganta harkokin ilimi.

Ya kuma kara da cewa zai yi dukkan kokari wajen ganin yaran Najeriya sun cimma burace-buracen da suke da shi a rayuwarsu.

Ranar yara: Tinubu ya yi kira ga iyaye

Shugaban kasar har ila yau ya taya iyayen yara, wakilansu da dukkan yan kasa kan zagoyowar ranar.

Bola Tinubu ya ce akwai bukatar iyaye su yi kokarin ba ƴaƴansu tarbiyya wajen cusa musu halayen gaskiya da rikon amana.

A cewarsa, idan aka rasa halayen da wahala a samar da gobe mai kyau. Saboda haka ya ce ko wane gida suyi kokarin ganin daura yaransu a kan turba mai kyau.

Shugaba Tinubu ya yi sauye-sauye

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauya shugabancin wasu hukumomin gwamnatin tarayya guda biyu.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Injiniya Chukwuemeka Woke da Dokta Adedeji Ashiru a matsayin waɗanda za su jagoranci hukumomin kasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading