Home Back

Halascin Yanke Farce Ko Aski Ga Wanda Ya Yi Niyyar Layya

leadership.ng 2024/6/26
Halascin Yanke Farce Ko Aski Ga Wanda Ya Yi Niyyar Layya

Yin aski ko yanke farce a goman farko na Zulhijja ba ya hana yin layya ko idan an yi ta zama karbabbiya ko ingantacciya, muddin mai layya ya cika sharuddan da shari’a ta ajiye a kan yin layyarsa, akwai sharudda a kan kansa, akwai sharudda akan layyarsa, akwai kuma sharudda akan dabbar.

Sharudda a kansa ya zama yana da iko na yin layyar, yanka kuma wajibi ne a yi ranar sallah bayan limamin da yake masu salla a garinsu ko a unguwarsu ya yanka dabbarsa, ko kuma ya bada izini kowa ya yanka layyarsa,duk wanda ya yanka dabbarsa kafin liman ya yanka tashi yankansa bai yiwu ba, ita kuma dabbar da za a yanka lallai ne ta zama daga cikin dabbobin ni’ima, wato Rakuma, Shanu, Tumakai da Awakai, kuma lallai ne dabbar ta zama ta cika shekarun girma jinsinta, kuma ba ta da nakasa ko wata illa kamar makanta ko gurguntaka ko rauni wanda yake fitar da jini bai warke ba.Muddin an cika wa’dannan sharuddan aka yi yankan nan to layya ta yi. Yin askin mai layya ko yanke farcensa bai shafi ingantuwar layyarsa ba ko rashin ingantuwarta.

Da yawa mutane su na daukar hadisin uwar Muminai Nana Ummu Salama wacce ta rawaito cewa; Annabi (SAW) ya ce, idan watan Zulhijja ya kama duk wanda yake da abin yanka wanda zai yanka a matsayin layya to kada ya yi aski ko yanke farce a wadannan kwanuka har sai ya yi layyarsa. Wannan hadisi an ganshi a cikin littafin Imamu Muslim.

Abinda muke jan hankalin mutane a kansa, litattafan hadisai musamman su manyan litattafai wato irinsu Bukhari da Muslim da sauransu abin da suka shardanta wa kansu cewa za su kawo dukkan hadisan da suka inganta cewa Annabi (SAW) ya fade su, amma ba su dora wa kansu ba yi wa mutane bayanin cewa wannan hadisi har yanzu yana aiki ko ba ya aiki, ko wannan hadisi akwai wani hadisin da ya dakatar da aikinsa ko ya rage fadin aikinsa ko ya kara fadin aikinsa, su dai kawai su na kawo hadisai ne ingantattu daga Annabi (SAW). Ba za ka iya gane cewa wannan hadisi har yanzu yana aiki ko ba ya aiki ba ko mene ne fadin ma’anarsa, ko me ake nufi da shi sai ka koma wajen malamai masana su ne za su yi ma wannan bayanin.

Kamar yadda a Alkur’ani za ka iya samun ayoyi tuli wadanda ga su nan har yanzu Alkur’ani ne ana karanta su amma kuma aiki da su an dakatar da shi. Bari mu ba da misalin guda daya. Fadin Allah (SWT) da yake cewa; Sura: 2 aya: 234, “Duk wadanda suka mutu daga cikinku suka bar matansu, matan za su zauna har tsawon wata hudu da kwana goma kafin su yi aure (wato zaman takaba ke nan).”

Sai ga wata aya ita kuma a cikin dai wannan sura: 2, aya: 240; Allah yana cewa; “Wadanda suka mutu daga cikinku suka bar mata ana ba matansu umarni zama tsawon shekara guda ba tare da fita ba kafin su yi aure.”

Dukkan wadannan ayoyi guda biyu ayoyi ne na Alkur’ani kuma har gobe ana karanta su,amma daya ta warware hukuncin daya, saboda haka dole ne daya za a dauka daga ciki, ba za a yi amfani da dayar ba.

Irin wadannan misalai suna da yawa a cikin Alkur’ani da hadisan Annabi (SAW). Shi ya sa wannan hadisi da muka fada a sama na uwar Muminai Ummu Salama Allah ya yarda da ita, hadisin Nana A’isha uwar Muminai Allah ya yarda da ita ya warware shi, inda take cewa;

Ita ce take shirya dabaibayi da igiyar daure dabbobin da Manzon Allah (SAW) zai yi layya da su ya aika su zuwa Harami, idan ya yi haka Annabi (SAW) bai taba hana kansa wani abu da Allah ya halatta mashi ba saboda dalilin ya yi niyyar zai yi layya. Shi ma dai wannan hadisi Imamu Muslim ne har yau ya rawaito shi, ta yadda za ka gane cewa Imamu Muslim yana kawo hadisai ne da suka inganta daga Annabi (SAW) ba yana aikin cewa wannan ana aiki da shi ko wannan ba a aiki da shi ba, kamar yadda aka rawaito hadisin da Annabi (SAW) aka tambaye shi a kan hukuncin wanda ya shafi azzakarinsa bayan ya yi alwala, Annabi (SAW) ya ba da amsar cewa azzakari wani bangare ne na jikin mutum saboda haka don mutum ya shafe shi alwalarsa tana nan, sai kuma ga wani hadisi shi kuma Annabi (SAW) yana cewa; Duk wanda ya shafi azzakarinsa bayan ya yi alwala to ya sake yin alwala.

Su ma wadannan hadisai guda biyu dukkansu Imamu Hajar Al-Askalani ya kawo su a cikin Albulugul Maram.

Saboda haka muke jan hankalin mutane da cewa yin aski ko yanke farce bai shafi hukuncin layya ba, ingancinta ko rashin ingancinta ba, suna nan a kan hukuncinsu. Akwai wasu malamai wadanda suke nuna cewa yin aski ko yanke farce dama ce ta mutum idan yana so ya yi idan kuma ba ya so sai ya bar shi, saboda ganin cewa idan an zo lissafa ladan da zai samu idan ya yi layya za a lissafa dukkan kwayar gashi da ta ke jikinsa, to idan ya aske su wai ba za a lissafa da su ba. To amma shi gashi ranar da aka aske shi washegari ma fitowa yake yi kuma wannan ba zai sa a ki lissafawa da shi ba.

Allah ya sa mu dace, amin.

People are also reading