Home Back

Ta’ammali da muggan kwayoyi na daga cikin matsalolin dake haifar da ɓarna a Najeriya – Marwa

premiumtimesng.com 2 days ago
Codein Girls
Codein Girls

Shugaban hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi ta kasa NDLEA Buba Marwa ya ce ta’ammali da muggan kwayoyi na daga cikin matsalolin dake haifar da ɓarna a kasa Najeriya.

Marwa ya fadi haka ne a taron wayar da kan matasa sannin illolin mu’amula da muggan kwayoyi a rayuwa.

Ya ce illolin dake tattare da muggan kwayoyi baya tsayawa akan wanda ke mua’mula ko fataucin su, yana shafan ‘yan uwa da abokan arziki, al’umma da kasa gaba daya.

Marwa ya yi kira ga matasa da su yi amfani da kuriciyar su domin gina kansu da ƙasa baki ɗaya.

Wacce ta shirya taron Hope Omeiza ta ce an shiyar taron ne domin wayar da kan matasa sanin illolin dake tattare da muggan kwayoyi tare da taimaka wa waɗanda shaye-shaye ya doɗe musu kwakwalwa a dalilin ta’ammali da muggan kwayoyi.

People are also reading