Gwamna Abba Na Kano Ya Dauki Sabon Matakin Yaki da Masu Safarar Miyagun Kwayoyi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta waiwayi dillalan miyagun kwayoyi, musamman wadanda ke neman mafakar shar'a yayin da aka kwace haramtattun kayansu.
Gwamna Abba Yusuf ya yi mamakin irin karfin halin wasu dillalan kwayar, wadanda ke zuwa kotu su karbo takardar izinin a saki kayansu da aka kwace.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafinsa na X ya ce gwamnan ya dauki mataki kan hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dawakin Tofa ya ce gwamnan Kano ya samu labarin abin da ke faruwa ne lokacin da ya ziyarci hukumar KAROTA domin ganin halin da take ciki.
Gwamna Yusuf ya yi mamaki matuka da ya ji cewa masu safarar miyagun kwayoyi na karbo takardun izinin kotu domin a saki kwayoyinsu da aka hukumar ta kwace.
Ya kuma yi mamakin yadda wasu alkalan jihar ke ba masu aikata laifin irin wannan takarda, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi.
A nan take, gwamnan jihar ya ba Antoni Janar na jihar umarni na yadda za a dakile masu safarar miyagun kwayoyi daga samun mafakar shari'a a nan gaba.
Ya kuma ce akwai bukatar saman da hadin kai tsakanin fannin shari'a da gwamnati domin ganin an dakile masifar da ke tattare da safarar miyagun kwayoyi.
Sanarwar ta kuma ce Abba ya ba hukumar KARATO umarni na yin duk mai yiwuwa wajen ganowa, kwacewa da kuma lalata miyagun kwayoyi a fadin jihar Kano.
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta amince da wani kudurin doka na yanke hukuncin kisa ga wadanda aka kama suna safarar miyagun kwayoyi.
Wannan kudurin ya samu goyon bayan mafi rinjayen sanatoci, yayin da dokar ke kokarin ganin an dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng