Home Back

Kaico: Wani Magidanci, Abdullahi Ya Kashe Matarsa Kan Ƴar Ƙaramar Gardama

legit.ng 2024/5/19
  • Ƴan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin halaka.matarsa kan wata ƴar gardama a Akure, babban birnin jihar Ondo
  • Binciken ƴan sanda ya nuna cewa magidancin, Fatai Abdullahi, ya caka wa matar almakashi ne kan faɗan da suka saba yi a koda yaushe
  • Mai magana da yawun ƴan sanda, Funmi Odunlami, ya ce yanzu haka suna tsare da wanda ake zargin kuma za su gurfanar da shi a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Wani magidanci ɗan kimanin shekara 30, Fatai Abdullahi, ya yi ajalin mai ɗakinsa mai suna Morenike kan wani ɗan ƙaramin sabani da ya shiga tsakanin su.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaiito, magidancin ya doka wa matarsa wani ƙarfe har rai ya yi halinsa a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
Wani magidanci ya daɓawa matarsa makami har lahira a jihar Ondo Hoto: Policeng Asali: Twitter

An tattaro cewa wanda ake zargin ya cakawa matar almakashi ne bayan wa+a ƴar gardama, wanda hakan ya zama ajalinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ƴan sandan jihar Ondo ta bayyana cewa magidancin ya aika wannan kisa ne tun ranar 27 ga watan Maris, 2024.

Mai magana da yawun hukumar ƴan sandan jihar, Funmi Odunlami, ya ce wata mata da ke zaune tare da ma'auratan ce ta kai rahoton lamarin.

"Ta faɗa mana cewa ta bar miji da matarsa a gida ranar 26 ga watan Maris, inɗa ta tafi ibada a coci amma da ta dawo da yammacin wannan rana, sai mijin ya sanar da ita ce matarsa ta mutu.
"Binciken farko ya nuna ma'auratan da yawan rigima da juna kak zuwada matar da take domin dubo ɗan da ta haifa a tsohon aurenta. Bayan ya kashe ta mutumin ya rufe hawarta a gida har sai da dare ya yi.
"Da aka zurfafa kan gawar matar an gano raunukan da aka mata ta hanyar soka mata wani abu a ciki da wuya. Sannan jami'ai sun gano almakashi cikin jini a wurin da aka yi kisan."

- Funmi Odunlami.

Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa yazu haka dai wanda ake zargin na hannun ƴan sanda kuma nan ba da daɗewa ba za a gurfanar da shi a gaban ƙuliya.

A wani rahoton kuma Ƴan sanda sun damƙe ƴan bindiga biyar bayan sun yi garkuwa da matar malamin coci da wasu mutum biyu a jihar Ondo.

Rahotanni sun nuna barci ne ya kwashe masu garkuwar har mutanen da suka sace suka samu nasarar arcewa ba tare da sun sani ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading