Euro 2024: Jadawalin fafatawar zagayen 'yan 16
Bayan kammala wasannin cikin rukuni a gasar kofin ƙasashen Turai, hukumar ƙwallon ƙafa ta Uefa ta fitar da jadawalin karawar zagayen sili ɗaya ƙwala.
Alhamis da Juma'a ranakun hutu ne a gasar, inda za a ci gaba da gumurzu ranar Asabar.
Ƙasashen da za su buga zagayen su ne:
Switzerland v Italy - Asabar, 29 ga watan Yuni (5:00)
Germany v Denmark - Asabar, 29 ga watan Yuni (8:00)
England v Slovakia - Lahadi, 30 ga watan Yuni (5:00)
Spain v Georgia - Lahadi, 30 ga watan Yuni (8:00)
France v Belgium - Litinin, 1 ga watan Yuli (5:00)
Portugal v Slovenia - Litinin, 1 ga watan Yuli (8:00)
Romania v Netherlands - Talata, 2 ga watan Yuli (5:00)
Austria v Turkey - Talata, 2 ga watan Yuli (8:00)
Duka lokutan agogon Najeriya ne da Nijar da Kamaru da Chadi.