Home Back

Hajj 2024: An Shiga Jimami Bayan Alhazai 2 Na Najeriya Sun Riga Mu Gidan Gaskiya

legit.ng 2 days ago
  • Allah ya yiwa wasu Alhazai biyu na jihar Kebbi, Hajiya Maryamu Mayalo da Alhaji Malami Besse na Koko Besse rasuwa
  • Marigayiya Hajiya Maryamu ta rasu ne a birnin Makka na Saudiyya yayin da Alhaji Malami ya rasu bayan ya dawo gida daga Saudiyya
  • Gwamnan jihar ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa bisa rasuwar Alhazan inda ya yi addu'ar Allah ya jiƙansu da rahama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Wasu Alhazai biyu daga jihar Kebbi, Hajiya Maryamu Mayalo da Alhaji Malami Besse na Koko Besse sun rasu.

Yayin da Hajiya Maryamu ta ƙaramar hukumar Maiyama ta rasu bayan doguwar jinya a Makka, Alhaji Malami ya rasu a Kebbi a ranar Lahadi jim kaɗan bayan dawowarsa daga Saudiyya.

Alhazai biyu na jihar Kebbi sun rasu
Alhazan jihar Kebbi mutum biyu sun rasu Hoto: Inside The Haramain Asali: Facebook

Wasu Alhazan jihar Kebbi sun rasu

Shugaban hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kebbi, Faruk Inabo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, Hajiya Maryamu Mayalo ta rasu ne a ranar Lahadi a asibitin Sarki Abdulazeez da ke birnin Makka, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Rasuwar Hajiya Maryamu da Alhaji Malami ya kai adadin Alhazan jihar Kebbi da suka rasu zuwa mutum biyar.

A Makonnin da suka gabata ne gwamnatin jihar ta sanar da rasuwar Tawalkatu Alako daga ƙaramar hukumar Jega, Abubakar Argungu da Muhammad Suleiman daga ƙaramar hukumar Argungu.

Gwamna Nasir ya yi ta'aziyya

"Gwamna Nasir Idris na miƙa ta'aziyyar rasuwar Hajiya Maryamu, ya kuma yi addu'ar Allah ya jikanta ya sanya ta a Aljanna Firdausi, ya ba iyalai da ƴan uwa haƙurin jure wannan babban rashin."
"Hakazalika, gwamnan yana miƙa ta’aziyyarsa ga hukumar jin daɗin Alhazai ta jiha, al’ummar ƙaramar hukumar Koko Besse da iyalan marigayi Alhaji Malami Besse na Koko Besse, wanda ya rasu ranar Lahadi da safe bayan ya dawo gida daga Saudiyya."

- Faruk Inabo

Alhazai 600 sun rasu a Saudiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla Alhazan ƙasar Masar 600 ne aka tabbatar da mutuwarsu a lokacin aikin Hajjin bana na shekarar 2024 a ƙasar Saudiyya.

Mutuwar Alhazan na da nasaba da tsananin zafin da aka sha fama da shi wanda ya kai ma'aunin celcius 51.8 a ranar Litinin, 17 ga watan Yuni 2024.

Asali: Legit.ng

People are also reading