Home Back

Mutuwar Jami’in Kwastam: Shugaba Tinubu Ya Aika Muhimmin Saƙo Ga Iyalan Etop Essien

legit.ng 2024/11/4
  • Shugaba Bola Tinubu ya ce ya kaɗu da jin labarin mutuwar wani mataimakin shugaban hukumar Kwastam, DC Etop Essien.
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ne ya fitar da sakon ta'aziyyar Tinubu a ranar Talata, 25 ga watan Yuni
  • Mun ruwaito cewa DC Etop ya yanke jiki ya fadi ne a yayin wani zaman ba da ba'asi kan gudanar da aiki a zauren Majalisar tarayya, Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi alhinin mutuwar mataimakin shugaban hukumar Kwastam, mai kula da sashen tattara haraji, DC Etop Andrew Essien.

Legit Hausa ta ruwaito cewa DC Essien ya yanke jiki ya fadi ne a zauren majalisar tarayya a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga kwamitin majalisar.

Shugaba Tinubu ya aika muhimmin saƙo ga iyalan Etop Essien
Tinubu ya jajantawa kwastan bisa rasuwar mataimakin kwanturola, Etop Essien. Hoto: Uche Nnadozie Asali: Facebook

Mutuwar jami'in Kwastam: Tinubu ya magantu

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan DC Etop, yana mai jimamin wannan rashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, shugaban kasar ya mika sakon ta'aziyya ga shugaban hukumar Kwastam na ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, da jami'an hukumar bisa rashin ma'aikacinsu.

Shugaban kasar na Najeriya ya yi addu'ar Allah ya jikan mamacin tare da ba iyalansa juriyar wannan babban rashi da suka yi.

Duba sanarwar a ƙasa:

Kwastam ta yi alhinin mutuwar DC Etop

A irin wannan yanayin ne shi ma shugaban hukumar Kwastam na ƙasa, Mista Adeniyi, a madadin ma'aikatan hukumar gaba daya ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan DC Etop.

Mista Adeniyi ya ce:

"Hukumar NCS ta kadu matuka da mutuwar wannan jajirtaccen jami'i. Muna a shirye wajen tallafawa iyalai da abokan aikin jami'in a yayin da suke makokin mutuwarsa."

Duba sanarwar a kasa:

Abubuwa uku game da DC Etop

A wani labarin, mun tattaro maku wasu muhimman abubuwa uku da ya kamata ku sani game da DC Etop Essien, jami'in Kwastam da ya mutu a zauren majalisar tarayya.

Daga cikin su akwai bayani kan yadda Etop Andrew Essien ya shafe shekaru sama da 30 yana aiki a hukumar NCS, kamar yadda rahoton hukumar ya nuna.

Asali: Legit.ng

People are also reading