Home Back

NLC Ta Bukaci A Kara Wa ‘Yan Jarida Albashi, Inshora Da Fansho

leadership.ng 2024/9/27
NLC Ta Bukaci A Kara Wa ‘Yan Jarida Albashi, Inshora Da Fansho

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) Kwamared Joe Ajaero, ya yi kira da a inganta albashi, inshora da kuma fanshon ‘yan jarida a fadin kasar nan.

Ajaero, ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ziyarci shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), Dakta Chris Isiguzo a Abuja.

Ya bayyana cewa ’yan jarida na taka rawar gani wajen fafutukar kwato ‘yancin kai da dimokuradiyyar Nijeriya, amma abun takaici ne yadda ake barin su, suna rokon a biya su albashinsu.

Shugaban na NLC, ya ce aikin jarida na ƙara muni a kowace rana, duk da cewar ana samun ingancin game da aikin.

“An yi watsi da jin dadin ‘yan jarida. Yayin da ’yan jarida rukuni ne na masu gwagwarmayar kwato ‘yanci

“’Yan jarida ba su da hutun karshen mako, ko hutu a lokacin bukukuwa. Suna aiki ta hanyar sanya wasu farin ciki.

“Akan kori dan jarida daga aiki ko a ki biyansa albashi na shekara daya, amma sauran ‘yan jarida ba za su wallafa labari kan irin wannan rashin adalci ba,” in ji Ajaero.

Ya kara da cewa: “Ina bayar da shawarar samar da yanayin da zamu ke tuntubar halin da suke ciki duk bayan shekaru biyu, don bayar da shawara ga ma’aikatan yada labarai don daidaita mafi karancin albashin ‘yan jarida.

“Kazalika, ya kamata a samu fansho mai gwabi ga dukkanin ‘yan jarida bayan sun yi ritaya daga aiki. Inshora wani abu ne da ya kamata ‘yan jarida su ji dadinsa.”

A nasa bangaren, Isiguzo ya ce kungiyar ta NUJ na yin kokari matuka wajen ganin an magance matsalolin da ‘yan jarida ke fuskanta.

People are also reading