Home Back

Bayan Matatar Man Dangote, Wani Kamfanin Mai Ya Rage Farashin Man Dizal

legit.ng 2024/5/12
  • Kamfanin mai na MRS Oil Plc ya rage farashin man dizal daga N1,700 zuwa N1,050 a dukkan gidajen mai mallakinsa a faɗin ƙasar nan
  • Kamfanin ya bayyana hakan ne kwanan nan inda kuma ya buƙaci ƴan Najeriya da su kai rahoton duk wani gidan mai da ke sayar da man fiye da sabon farashin
  • Matakin ya biyo bayan zaftare farashin man dizal da matatar man fetur ta Dangote ta yi zuwa Naira 980 kan kowace lita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kamfanin mai na MRS Oil Plc ya zaftare farashin man dizal zuwa N1,051 a faɗin gidajen mai mallakinsa a faɗin Najeriya.

Bayanin hakan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar wacce ta yi yawo a kafafen sada zumunta.

Kamfanin MRS ya rage farashi
Kamfanin mai na MRS ya rage farashin man dizal Hoto: Bloomberg/Contributor Asali: Getty Images

MRS ya rage farashi daga N1,700 zuwa N1,050

Kamfanin ya rage farashin man dizal ɗin ne daga N1,700 kan kowace lita bayan matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin man dizal ɗin, cewar rahotpn jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, mahukuntan kamfanin na MRS sun buƙaci jama'a da su kai rahoton duk wani gidan mai wanda yake siyar da man dizal fiye da farashin da ya ƙayyade, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Yanzu muna sayar da man dizal a dukkan gidajen mai na MRS a Najeriya kan farashin N1,050 kan kowacce lita.
"A taimaka a kai rahoton duk gidan man da ba ya sayarwa kan wannan farashin ga ɓangaren kula da abokan cinikayya ko masu fallasa."

Farashin man dizal zai karye

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya ta ce tana sa ran cewa matatar man Dangote za ta kara rage farashin dizal din ta zuwa Naira 700 kan kowace lita.

Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN na ƙasa, Hammed Fashola ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai.

Hammed ya kuma yabawa matatar man Dangote bisa rage farashin man dizal daga sama da Naira 1,200 zuwa N1,000 a kan kowace lita.

Asali: Legit.ng

People are also reading