Home Back

Kalubalen Da Manyan Kafafen Labarai Ke Fuskanta A Yanzu – Shugaban MacArthur

leadership.ng 2024/5/2
Kalubalen Da Manyan Kafafen Labarai Ke Fuskanta A Yanzu – Shugaban MacArthur

A makon da ya gabata ne, Shugaban Gidauniyar ‘MacArthur Foundation’ KOLE SHATIMA, ya zanta da wakilinmu IDRIS UMAR ZARIYA a kan halin da gidajen jaridu suke ciki da su kansu ‘yan jaridar tare da tsokaci a kan ayyukan gidauniyar mai ofisoshi a Chikago ta Amurka, da Delhin Indiya da kuma Abujar Nijeriya. Ga yadda ta kasance:

Masu karatu za su so jin shin da wa suke tare a daidai wannan lokaci?

Sunana Kole Shatima, ni ne kuma Shugaban ‘MacArthur Foundation’, mai ofis a Chicago da Kasar Indiya da kuma nan Abuja Nijeriya.

Wadane irin ayyuka wannan gidauniya da ka ke shugabanta ta ke yi wa al’umma?

Gidauniyar ‘MacArthur Foundation’, tana bayar da gudummawa a bangarori da dama, musamman a bangaren yada labarai, wato gidajen jaridu, Talabijin har ma da Rediyo; muna ba su tallafi, domin su rika fitar da rahotanni ko labarai masu inganci, wanda zai wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma.

A jerin gidajen yada labarai, wanda wannan gidauniya ta bai wa ire-iren wannan tallafi, akwai kamar BBC, Daily Trust, Arewa 24 da sauran makamantansu. Har ila yau, misali ka ga yanzu haka ana gudanar da babban taro na kasa a nan Jami’ar Ahmadu Bello, wanda ganin muhimmancin taron ne ya sa muka shigo, domin bayar da gudunmawarmu, sakamakon gabatar da taron da za a yi a kan yada labarai cikin tsaro a zamanin da muke ciki na ci gaban rayuwa.

Yaushe kuka fara wannan kokari na tallafa wa kafafen yada labarai, sannan wane sakamako kuke bukata?

To gaskiya mun kai shekara takwas da farawa, sannan kuma daga cikin bukatun da muke nema su ne: Da yake yanzu komai ya canza, gidajen jaridu babu wata riba da suke samu sakamakon ci gaban da ake samu na zamani, misali da yawan masu amfani da yanar gizo (social media) wajen aiwatar da tallace-tallacen hajarsu, sun fi masu manyan kamfanonin gidajen jaridu samun kudin shiga.

Wannan dalili ne ya sa muka ce in har ba a so gidajen jaridu su yada rahotannin karya, wato rahoton da zai tayar da hankali, wajibi ne a taimaka musu; domin kuwa hakan ne zai kare su daga yada rahotannin da ba na gaskiya ba. Ma’ana, bayar da tallafi ne zai sa a sanya rahoto mai inganci, wanda mu kuma hakan shi ne muradunmu, shi muke so ya tabbata a koda-yaushe.

Har ila yau dalilinmu shi ne, idan aka bar gidajen jaridu babu wani mai taimakon su a irin matsalar rashin kudin shiga da ake fama da shi yanzu, ko shakka babu mahukunta za su iya amfani da wannan dama su saye gidajen, domin buga musu irin abin da suke so; wanda hakan ko kadan bai dace ba.

Me ya kamata a yi a irin wannan hali da ake ciki?

Gaskiya abin da ya kamata a yi shi ne, taimakon gidajen jaridu tare da bai wa su kansu ‘yan jarida kulawa ta musamman wajen gudanar da ayyukansu. Hakan ne zai sa a rika tantance rahotanin da aka samu kafin a watsa su ga daukacin al’umma.

Wane kira za ka yi ga su kansu ‘yan jarida masu zuwa neman rahotanni a cikin  l’umma babu dare ba rana?

Kiran da zan yi ga ‘yan jarida shi ne, don Allah kafin su saki kowane irin labari, su tabbata sun tantance shi yadda ya kamata, don gudun tayar da fitina a cikin al’umma; ma’ana dai su rika jin dukkanin bangarori biyu kafin su kai ga watsa shi.

Sannan, idan ya zama dole sai an saki labara; to a tabbatar da cewa an fadi gaskiya, ka da a fadi karya. Abu na biyu kuma da zan bai wa ‘yan jarida shawara a kai shi ne, su guji sanya banbancin addini a yayin gudanar da ayyukansu, domin kuwa aikin jarida bai gaji haka ba ko kadan.

A karshe, wace shawara za ka bai wa gwamnati kan yadda ‘yan jarida ke gudanar da ayyukansu a nan Nijeriya?

A nan, shawarata ga gwamnati ita ce, ya kamata ta rika sanar da ‘yan jarida halin da take ciki, hakan zai taimaka wajen fitar da rahotannin gaskya. Abu na biyu kuma shi ne, ya kamata gwamnati ta kula da hakkin ‘yan jarida komai kankantansa, domin kuwa hakan zai taimaka wajen samar da labarai masu inganci a cikin al’umma, domin su ma ‘yan jaridar suna da ‘yanci cikakke ba bayi ba ne.

Ko kana da wani abin cewa wanda ban taMbaye ka ba?

Kwarai kuwa akwai shi, ina so na yi amfani da wannan dama, don yin jinjina ga sashen koyar da ilmin yada labarai na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, (Mass Communication Department) da shugaban sojoji; Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, bisa yadda ya bayar da gudunmawarsa da kuma mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambassada Ahmed Nuhu Bamalli da Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Kabir Bala da daluban sashin koyar da aikin jarida da kuma dukkanin ma’aikatanmu na ‘MacArthur Foundation’ da suka halarci wannan taro na karawa juna sani, a kan kalubalen da ake fuskanta a bangaren yada labarai a sashin tsaro tare da neman mafita mai inganci.

Haka zalika, na ji dadi matuka da gudunmawar da gidauniyar tamu ta bayar; muna alfari da hakan kwarai da gaske tare da fatan za a ci gaba da samun irin sa a tsakanin al’umma.

People are also reading