Home Back

Sabuwar dokar zama 'dan kasa a nan Jamus ta fara aiki

dw.com 2024/10/6
Hoto: Wolfgang M. Weber/IMAGO

A Alhamis din nan ce sabuwar dokar zama 'dan kasa a nan Jamus ta fara aiki, wadda ta saukaka hanyoyin samun Fasfo din kasar ga duk mai nema, sannan kuma ya ci gaba da rike na kasarsa ta asali da ya fito.

Karin bayani:Jamus: Dokokin mallakar fasfo ga baki

Tanadin dokar ya bai wa mazaunin Jamus na tsawon shekaru 5 damar mallakar shaidar zama 'dan kasar matukar ya cika dukkan ka'idojin da aka nema, maimakon shekaru 8 da dokar ta ce a baya.

Haka zalika yaran da aka haifa a Jamus za a ba su damar zama Jamusawa idan har daya daga cikin iyayensu ya shafe shekaru 5 yana zaune a kasar, maimakon shekaru 8 a baya.

Wani karin tagomashi na dokar shi ne mutum ka iya samun izninin zama 'dan kasa a cikin shekaru 3 kacal, ta hanyar nuna himma da halin kirki a makaranta ko wurin aiki, ko ma wani wurin da yake.

People are also reading