Home Back

Girman Darajar Manzon Allah (SAW) Da Allah Ya Yi Rantsuwa Da Ita (5)

leadership.ng 2024/5/2
Girman Darajar Manzon Allah (SAW) Da Allah Ya Yi Rantsuwa Da Ita (5)

‘Yan’uwa assalamu alaikum warahmtullahi ta’ala wa barkatuhu. Har yanzu dai muna nan a cikin bayanin rantsuwar da Allah ya yi da darajojin shugaban halitta, Annabi Muhammad (SAW) inda a makon jiya muka kwana a bayani kan abubuwan da muke imani da su ba tare da dora wa kanmu cewa dole sai mun gano abin ba. Kuduri ne kawai za mu yi sai mu yi imani a zuciya.

Haka nan zaman Arfa, wani wuri ne muke zuwa mu zauna kawai, a nan za mu yi Sallar Azahar da La’asar amma kuma ba a so mu yi Sallar Magriba da Isha’i a wurin don ma kar mu zaci ko wannan ne silar da ta sa aka ce mu je wurin, dole sai mun tafi Muzdalifa kafin mu karasa sauran sallolin.

Abin da ake so kawai mu je Arfa mu zauna kuma wannan zaman shi ne Hajji baki daya kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce, “Arfa ita ce Hajji”.

Ka ga duk a rin wannan sai dai bin umurni ne kawai, walau mun gane hikimar da ke ciki ko ba mu gane ba. Ba kowane Musulmi ne zai ce ya san duk dalilan da Allah ya ce a yi wadannan ibadun ba, don haka ko mutum ya gane ko bai gane ba ya aikata kawai saboda dalilin cewa Allah ne ya umurci a yi. Kamar dai yadda soja yake, idan ya ba da umurni ba za a tsaya tambayar dalili ba, za a aikata ne kawai sai in daga baya tukuna bayan an gama sai a tambaya. Saboda haka a cikin aikin ibadu da aka ce mu yi, ba sai mun san dalili ba, mu Allah muke bi, tunda ya ce a yi, mu aikata kawai ko mun san dalilin ko ba mu sani ba.

Haka nan ko a cikin kudurcewar ma akwai abin da mun yi imani da shi, ko mun iya ganewa ko ba mu iya ba. Manzon Allah (SAW) ya ba mu labari daga Allah ne kuma mun yarda mun yi imani da shi kamar mun gani. Misali, Manzon Allah ya ba mu labarin akwai wata irin gada a lahira sunanta Siradi, a kan wuta za a shimfida ta, ta fi silin gashi siriri, ta fi takobi kaifi, kuma duk halitta za ta bi ta kanta, wannan gada kuwa wace iri ce? Amma kuma lallai mun yarda akwai ta mun yi imani da ita. Duk wanda bai yi imani da ita ba sai Shari’a ta caje shi da laifin rashin imani. To irin wannan imani ne kawai ake kudurcewa a zuciya. Kamar yadda labarin gadar nan ta Siradi take, haka ma akwai wasu maganganun Allah a cikin Alkur’ani da ya saukar wanda sai dai imani kawai, amma ba mu san ma’anarsu ba. Yana daga cikinsu wadannan rantsuwa da Allah ya yi da Alif Lam Miym. Malamai masu Tafsiri karshen abin da suke fassarawa da shi shi ne “Allah ne ya fi sanin abin da yake nufi da wannan”. Sai dai, Malaman da Allah ya haskaka musu sukan yi tawili kawai. Ma’anar tawili kamar mu a Hausa, wani ya zo ya ce “wane ya ci mun mutunci”, ma’anarsa ya bata masa suna. Ko a ce “wane ya yi mun yankan kauna”, ma’anar zancen shi ne mutum ya zaci zai iya sa wani ya aikata wani abu ko ya hana shi amma sai ya ki. A nan duk, maganganun da aka fada a zahiri sun saba da ma’anoninsu na ainihi. Wasu masana kuma za su iya fassara wadannan zantukan da wani abu daban. Kamar misali, idan aka ce “wane ya yi mun cin mutunci” ana nufin an kawo abinci ga wani mutum (kamar bako) sai ya ci dan kadan ya ce ruwa kawai yake so, to a nan sai a ce ya yi cin mutunci. Ko kuma idan aka ga yara suna cin abinci suna wawaso sai a ce “kai ku bari; ku yi cin mutunci”. A bangaren “Yankan kauna” kuma, a wata fassarar kamar a ce mutum ne ya sayi ragonsa na sunan jaririn da matarsa ta haifa, kawai sai ya yi bako kafin ranar sunan sai ya umurci a yanka wa bakon nan ragon, a nan sai a ce “wane ya yi mun yankan kauna”. Duk wadannan suna da ma’anarsu da ta fito a zahiri mutane suka san ta; sannan suna da ma’anarsu da ta dan buya sai masanan abin za su bayyana.

Kamar yadda misalin Hausa nan yake, haka nan karatun da muke karantawa ma’anarsa take. Fassarar zahirin tana nan amma kuma akwai malaman da Allah ya haskaka musu suka fahimci wata ma’anar daban, kamar yadda wasu suka riki cin mutunci ba a matsayin zagi ba ko yankan kauna a matsayin kunyatawa.

To Allah (SWT) a cikin rantse-rantsen nasa, akwai wadda ya yi da harafi akwai kuma wadda ya yi da kalma. Kamar su “Saad”, “Kaaf”, “Nuun”, duka wadannan haruffa ne dai-dai. Na kalmomi kuma su ne kamar “Wannajmi”, “Wal’asri” da sauran su. Sannan Allah ya yi rantsuwa da haruffa biyu-biyu irin su “He miym”, “Da ha”, haka nan da kalma biyu-biyu kamar “Wadduhe. Wallaili izha saje”, “wassama’i waddarik”. Sai kuma rantsuwa da harafi uku-uku, kamar “Alif Lam Miym” da muka yi bayani a sama. Na kalmomi uku kuma kamar ayoyin ukun farkon Suratus Saafaat. Akwai wuraren da Allah ya rantse da haruffai hudu-hudu, kamar “Alif Lam Miym Saad” da kuma wurin da ya rantse da kalmomi hudu kamar ayoyi hudun farkon Suratuz Zariyati. Har ila yau, akwai inda Allah ya rantse da haruffa guda biyar, kamar “Kaaf Haa Yaa Ain Saad” da “He miym Ain Siyn Kaaf”, sannan akwai na kalmomi biyar kamar daga “wadduur wa kitaabin masduur…” ko “Walmursalati urfa fal’asifaati asfa… “Wannazi’ati garka wannashidaati nashda….” har zuwa kan na biyar-biyar din ayoyin. Gaba dayan rantse-rantsen su 28 ne, kuma ikon Allah, Allah ya raba su rabi-rabi, na haruffa sau 14; na kalma ma sau 14. Na kalmomi ana sanin ma’anarsa amma na haruffa sai dai a ce “Allah ne mafi sanin abin da yake nufi da su”. Amma kuma ga Sahabbai da sauran Waliyyan Allah sun fadi ma’anarsu kamar yadda Allah ya haska musu tawilinsu wanda idan mutum ya dauka sai ya amfanu kuma ya amfanar.

People are also reading