EFCC Ta Bankado Badakalar N2.17b a Lokacin Gwamnatin Goodluck Jonathan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Hukuma mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bankado badakalar kudi da ya faru lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.
Hukumar EFFC ta bayyana a shafin ta na Facebook cewa badakalar ta faru ne karkashin ofishin mai ba shugaba Jonathan shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki.
Tun a shekarun baya dai hukumar EFCC ta gurfanar da Sambo Dasuki bisa karkatar da kudin makamai wanda har hakan ya kai shi ga zaman gidan yari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC ta gurfanar dan kwangilar da ta kama mai suna Olugbbenga Obadina a ranar Litinin 20 watan Mayu.
Dan kwangilar ya tabbatar wa kotu cewa ya karbi zunzurutun kudi N2.17b daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a shekarar 2015.
Har ila yau a zaman kotun, dan kwangilar ya bayyana cewa ya karbi kudin ne ba tare da manufar gudanar da wani aiki ga gwamnatin tarayya ba.
Ya kuma ƙaryata rade-radin da ke cewa an ba shi kudin ne domin ayyukan samar da wuta ta hanyar amfani da hasken rana a jihar Yobe.
Bayan sauraron karar da yin tambayoyi da wanda ake zargi, alkalin kotun mai Shari'a Nnamdi Dimgba ya daga shari'ar.
A ranar 30 ga watan Mayu kotun za ta zauna domin cigaba da sauraron karar da EFCC ta shigar kan zargin dan kwangilar da aikata laifuffuka takwas.
A wani rahoton, kun ji cewa Ola Olukoyede ya sha alwashin cewa zai yi murabus daga kujerar shugaban EFCC idan aka gaza gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu.
Shugaban EFCC ya kuma rantse da cewa zai bi diddigin shari'ar tsohon gwamnan jihar Kogi har zuwa lokacin da za a ƙarkare ta domin tabbatar da gaskiya.
Asali: Legit.ng