Home Back

Ana Fama da Rigimar Sarauta, Gwamna Abba Ya Jiƙa Wa Wasu Yan Kasuwa Aiki a Kano

legit.ng 2024/7/2
  • Gwamnatin Kano ta umarci ƴan kasuwa su tashi daga wuraren da aka kebe domin shakatawa da hutawa a faɗin jihar
  • Kwamishinan mahalli da sauyin yanayi, Nasiru Sule Garo, ya ce mutane sun mayar da wasu lambunan shaƙatawa wurin kasuwanci ba tare da izini ba
  • Ya ce a yanzu gwamnati ta shirya gyara irin waɗannan wurare kuma za ta shuka itatuwa domin samar da isasshiyar iskar Oxygen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta waiwayi wasu wuraren da aka ware domin hutawa da shaƙatawa a jihar.

Ƴan kasuwa sun mamaye irin waɗannan wurare da aka keɓe domin masu hutawa ko shaƙatawa, sun mayar da su wurin hada-hadar kasuwanci.

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnatin Kano ta tashi yan kasuwa a wuraren hutawa da shakatawa Hoto: Abba Kabir Yusuf Asali: Facebook

Sai dai a halin yanzun, Gwamnatin Abba ta umarci dukkan ƴan kasuwar da suka karɓe irin waɗannan wurare su tattara kayansu su tashi, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na Kano, Nasiru Sule Garo, ne ya ba da wannan umarni ranar Laraba yayin bikin ranar muhalli ta duniya.

Garo ya ce akwai da yawa daga cikin irin wadannan lambuna da wuraren shakatawa na gwamna a Kano wadanda ‘yan kasuwa suka mamaye.

A cewarsa, yanzu gwamnati ta dawo kansu, kuma ta shirya gyara su domin a ci gaba da amfani da su a matsayin lambunan shaƙatawa da hutawa.

Kwamishinan ya ce lambun daura da asibitin Abdullahi Waste da kuma wani da ke kan titin Audu Bako an mayar da su wuraren kasuwanci sabanin dalilin kafa su.

Ya ƙara da cewa a wani bangare na aikin dashen itatuwa domin dakile sauyin yanayi, gwamnatin jihar na shirin shuka iri miliyan uku tare da hadin gwiwar ACRSaL da masu ruwa da tsaki.

"An canza sunan ma’aikatar zuwa Ma'aikatar Muhalli da sauyin yanayi domin tunkarar matsalolin sauyin yanayi na duniya kamar yadda ya shafi Kano."

Garo ya ce baya ga tsaftace magudanar ruwa da matakan daƙile zaizayar kasa, ma’aikatar ta yi feshin magance sauro da kwari a kananan hukumomi 44.

Gobara ta kashe mutum 8 a Kano

A wani rahoton kuma an rasa rayukan mutum takwas kuma kadarorin da suka kai na N31.6m sun salwanta a ibtila'in gobara a jihar Kano cikin watan Mayu.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi ne ya faɗi haka da yake jawabi kan ayyukan hukumar a watan jiya.

Asali: Legit.ng

People are also reading