Home Back

HAJJ: MANYA-MANYA IN JI ƘANANA: Za a fara jigilar Alhazan Kaduna da ta fi kowacce jiha yawan maniyyata a bana

premiumtimesng.com 2024/9/27
Hajji
Hajji

Hukumar Alhazai ta Kasa ta bayyana cewa daga ranar Laraba za a a fara jigilar maniyyata aikin Hajji na bana daga Jihohin Kadkuna, Sokoto, Kano, Barno, Yobe da Adamawa.

Kakakin hukumar NAHCON Fatiima Usara ta bayyana haka a wata sanarwa ranar Talata in da ta bada ƙarin haske game da tashi da saukar Maniyyatan Najeriya a bana.

Jihar Kaduna ce ta fi kowacce jiha yawan maniyyata a bana da maniyyata akalla 4,600 wanda za su aikin haji a bana daga jihar.

Jihar Sokoto ce ke bi mata da maniyyata 3500 sai jihar Kano dake maniyyata 3100.

An Kammala jigilar Alhazan jihar Nasarawa

A cikin sanarwar NAHCON ta bayyana cewa an kammala jigilar Alhazan jihar Nasarawa wanda suka tashi da Babban Birnin Tarayya, Abuja sannan maniyyata rundunar sojoji ma za su kammala tashi zuwa kasa mai tsarki ranar Talata da dare.

Bayan haka kuma Usara ta bada karin bayani game da matsalar raba kuɗin guziri na maniyyata, inda ta ce tuni an warware wannan matsala,

” An warware wannan matsala, duka maiyyatan Najeriya da zasu yi aiki a bana, za su karbi kuɗin guzirin su Dala $500 maimakon raba musu kuɗi da kati.

Zuwa yanzu hukumar NAHCON ta yi jihilar maniyyata sama da 12,000 zuwa ƙasa mai tsarki a tashin jirage 30.

A ƙarshe ta ce a kamar yadda aka saba, idan an kammala aikin Hajji, dawowa zai faro ne da waɗanda suka fara tashi.

People are also reading