Bikin al'adun Yarabawa da Burna Boy cikin hotunan Afirka
Zaɓɓaɓun ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan Nahiyar a wasu sassan duniya
Wasu mata sanye da anko a wajen bikin al'adun yarabawa a Najeriya ranar Talata.
Bikin al'adun girmamawa ne ga sarkin yarabawa Awuja Ile na yankin Ijebu.
Wasu ƴan rawa a ranar Lahadi a Afirka ta Kudu a lokacin da suke jiran a basu damar yin rawa a wajen taron tinawa da juyin juya halin ɗalibai na Soweto.
Mutane na gudanar da wannan muhimmin biki domin tunawa da kisan kiyashi da ƴn sanda suka yi wa ɗaliban da ke gudanar da zanga-zangar lumana don nuna adawa da mulkin wariya a ƙasar.
Lokacin da shahararren mawaƙin Najeriya Burna Boy da shahararren ɗan ƙwallon ƙafa Didier Drogba suke nunawa juna ƙauna a Faransa ranar Talata a wajen taron bajen kolin kamfanin kayan ƙawa na Louis Vuitton
Yadda aka yi zanga-zangar nuna adawa da sabon haraji da gwamnatin ƙasar ta ƙaƙabawa ƴan ƙasar, yayin da ƴan sanda suka kama gwamman masu zanga-zangar.
Sarki Eswatini King Mswati III da matarsa a wajen taron rantsar da Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban ƙasar Afirka ta Kudu a karo na biyu.
Wurin da ake rina kaya a Shuvvara Tannery na ƙasar Morroco
A ranar Juma'a, a lokacin da aka ceto wannan yaron daga ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a Abidjan babban birnin ƙsar Ivory Coast
Ana kaɗa wa Faith Kipyegon ganga a lokacin da take tseren mita 5,000 ta mata a shirye-shiryen zaɓar waɗanda za su wakilci Kenya a wasannin Olympics da za a yi a birnin Paris a watan gobe.
Wannan yaron na farin ciki ne sakamakon alawa da balan-balan da aka bashi a lokacin bikin babbar sallah a ranar Lahadi a birnin Kamfala na ƙasar Uganda.
Wasu mata kenan a birnin Dakar na Senegal a ranar sallah.