Home Back

'Rashin riga-kafi na jefa yara cikin haɗari'

bbc.com 2024/5/10
baby immunize

Asalin hoton, Getty Images

Ana gudanar da gangamin makon riga-kafi na duniya inda ake wayar da kai game da muhimmancin yi wa yara riga-kafin cutukan da za a iya yakarsu ta hanyar riga-kafi.

Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware makon karshe na watan Afirilun kowace shekara inda aka fara gangamin a ranar Laraba a matsayin makon riga-kafi don sake fito da muhimmancin riga-kafin da ake yi wa yara kanana.

Ana gudanar da wannan gangamin wayar da kan jama’a ne don su kara fahimtar muhimmancin yi wa yara riga-kafi daga ranar 24 zuwa 30 ga wannan watan na Afirilu.

Masana na cewa yi wa jarirai allurar riga-kafin na kare su daga cutuka da dama ciki har da sarke hakora da kyanda.

Dr Halima Adamu Dal likitar yara ce kuma shugabar kungiyar likitoci mata ta jihar Kano ta ce daga zarar an haifi yaro ana son a ba shi allurar riga-kafin da za ta ba shi kariya daga tarin fuka da cutar hanta da kuma Folio saboda su wadannan cuttuka suna nan a kodayaushe yaron zai iya kamuwa da su nan take, in ji ta.

Bayan sati shida ma akwai wadda ake bayarwa daga nan sai sati 10 sai kuma 14, daga nan sai kuma wata shida, da wata tara inda ake ba da riga-kafin kyanda da sinadarin bitamin A, idan yaro ya kai wata 15 za a ƙara masa ta kyanda, cewar Dr Halima.

To sai dai duk da muhimmanci da riga-kafin ke da shi, har yanzu akwai al’ummomin da ba sa bayar da hadin kai a yi wa ‘ya’yansu, al’amarin da Dr Halima ke cewa yana jefa yara cikin hadari.

Likitar ta ce ƙalubalen da ɓangaren ke fuskanta shi ne, akwai riga-kafin a ƙasa amman mutane ba sa zuwa saboda suna ganin kamar tana da illa ga yara.

Sannan ya kamata a samar da ita ko ina domin ana son ana haihuwar yaro a yi masa.

Dr Halima ta kara da cewa nan gaba a cikin wannan makon za su shirya taruka, inda za a kara fadakar da likitoci da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki mahimmancin bai wa yara cikakkun alluran riga-kafi tun daga haihuwa har zuwa watanni 15.

Sannan da neman gwamnati ta kara cibiyoyin da ake riga-kafin cutukan yara a lungu da sako.

Dr Halima ta yi kira ga iyaye da su taimaka su riƙa kai 'ya'yansu allurar riga-kafi saboda tana da matukar mahimmanci, kuma ya kamata ana tambaya kan duk abun da ba a gane ba kan ta, in ji likitar..

Bayanai na cewa riga-kafi kan kare miliyoyin yara daga kamuwa da cututtuka a kowacce shekara, kuma shi ne matakin farko da ke kare yaduwar cututtuka a tsakanin al’umma, wanda masu iya magana ke cewa riga-kafi ya fi magani.

People are also reading