Home Back

Karin Albashi: 'Don Allah Kuyi Hakuri Ku Karbi ₦60,000’ Gwamnati Ta Roki Yan Kwadago

legit.ng 2024/7/1
  • A yau Laraba gwamnatin Najeriya ta mika kokon bara ga kungiyar kwadago game da karin mafi ƙarancin albashin ma'aikata
  • Rokon da gwamnatin ta yi ya biyo bayan baran-baran da kungiyar ta yi da gwamnatin a wani taro da suka yi kan karanci albashi
  • A halin da ake ciki kungiyar kwadago ta nemi ₦494,000 ya zama mafi ƙarancin albashi, ita kuma gwamnati ta tsaya a kan ₦60,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Gwamnatin Najeriya ta roki kungiyoyin kwadagon NLC da TUC su kai zuciya nesa a tattaunawar da suke game da mafi ƙarancin albashi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ce ta roki kungiyar a madadin gwamnatin.

Kwadago
Gwamnati ta roki yan kwadago kan karancin albashi. Hoto: @DOlusegun Asali: Twitter

Tun farkon gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ake kai komo tsakanin yan kwadago da gwamnatin tarayya kan karin kudin amma an kasa samun matsaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tattaunawar gwamnati da ma'aikata kan albashi

A jiya Talata kungiyar kwadago ta zauna da gwamnatin tarayya domin samun matsaya a kan mafi karancin albashin ma'aikata.

Sai dai sun tashi baran-baran yayin da kungiyar kwadago ta nemi a biya ₦494,000 ita kuma gwamnati ta yi mata tayin ₦60,000.

Albashi: Kiran minista ga yan kwadago

Bayan sun kasa cimma matsaya a jiya Talata, ministar kwadago ta roki kungiyar da su nuna kishin kasa wajen amicewa da ₦60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Ministar ta ce ya kamata 'yan kwadago su fahimci cewa har yanzu Najeriya ba ta farfaɗo daga matsalolin tattalin arziki ba, rahoton Vanguard.

Minista ta roki a dawo teburin tattaunawa

Har ila yau, ministar ya roki kungiyar kwadago kan dawowa teburin tattaunawa domin samun mafita.

Ta ce tattaunawar da suka fara yana da muhimmanci wajen samun daidaito kan kudin da zai wadatar da ma'aikatan Najeriya.

NLC ta nemi a biya ma'aikata N500,000

A wani rahoton, kun ji cewa a kwanakin baya kungiyar kwadago ta nemi N500,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan Najeriya.

Kungiyoyin kwadago, gwamnonin jihohi, ministoci, kungiyoyin farar hula ne za su yanke hukunci kan sabon mafi karancin albashin da ake nema a fara biya.

Asali: Legit.ng

People are also reading