Home Back

Rudin Soyayya: Rundunar Sojin Najeriya Ta Tabbatar da Jami’inta Ya Kashe Mace Mai Ciki

legit.ng 2024/5/20
  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa ta dauki tsohon da Boko Haram aiki bayan an fara yada jita-jita
  • Ta tabbatar da yadda soja daga cikin jami’anta ya kasha wata mata bayan samun sabani a tsakaninsu
  • Rundunar ta tabbatarwa ‘yan Najeriya za ta ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da tsaro da yiwa kowa adalci

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan wata mata da wani jami’inta ya yi a barikinta da ke jihar Enugu a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

A makon da ya gabata ne aka samu rahoton cewa, Muhammad Adamu, wanda aka ce tubabben dan Boko Haram ne da ya shiga aikin soja ya kashe wata mata a barikin Sojan Najeriya na 82 da ke jihar.

Sojoji sun amsa jami'insu ya kashe mata mai ciki a Enugu
Rundunar soji ta amsa jami'inta ya kashe wata mata a Enugu | Hoto: @DefenceInfoNG Asali: Twitter

Matar mai suna Hauwakulu Tabra, an ce budurwar Adamu ce. An ce tana dauke cikin da wani ya yi mata, wanda hakan ya fusata sojan, Premium Times ta ruwaito.

Rundunar sojin Najeriya ta yi martani

Da yake martani kan lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama Adamu tare da tuhumarsa da aikata kisan kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nwachukwu, ya ce ana zarfin Adamu da kashe matar ne a daren Alhamis kuma an gano gawarta a cikin harabar barikin a ranar Juma’a.

A cewarsa:

“Bincike na farko ya nuna cewa sojan ne ya kashe marigayi Hauwakulu Tabra, wanda a yanzu haka yake tsare don ci gaba da bincike tare da gano dalilin da ya sa ya aikata hakan.”

Adamu ba tsohon dan Boko Haram bane, inji soji

Sai dai, kakakin rundunar ya musanta ikirarin cewa Adamu dan Boko Haram ne da ya tuba, rahoton The Guardian.

Daga nan, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan Hauwakulu tare da bayyana jimamin abin da ya faru.

Kakakin ya kuma tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa za a yi adalci a lamarin domin rundunar ba za ta lamunci duk wani dabi’a ta rashin da’a a cikin jami’anta ba.

Soja ya sha alwashin daukar fansa kan kashe abokan aikinsa

A bangare guda, wani soja mai suna Egitanghan G. ya bayyana cewa za su dauki fansa kan kisan sojoji da aka yi a jihar Delta.

Sojan wanda shi ma ya fito daga jihar Delta ya ce abin takaici ne yadda wasu ke munanan kalamai ga sojojin da suka mutu.

Egitanghan ya nuna damuwa kan yadda abin ya faru duk da sadaukar da rayukansu da suke yi wurin kare kasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading