Home Back

SHIRIN BUNƘASA NOMAN ZAMANI: Gwamnatin Jigawa ta ƙulla haɗin gwiwa da kamfanonin Amurka biyu, za su shigo da taraktoci 300

premiumtimesng.com 2024/5/19
SHIRIN BUNƘASA NOMAN ZAMANI: Gwamnatin Jigawa ta ƙulla haɗin gwiwa da kamfanonin Amurka biyu, za su shigo da taraktoci 300

A ƙoƙarin da Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ke yi wajen ganin jihar ta yi fice a fannin bunƙasa harkokin noma na zamani, gwamnan ya cimma wata gagarimar ƙulla ƙawancen haɗin gwiwa da manyan kamfanonin bunƙasa noman zamani na Amurka, wato John Deere da kuma Tata International.

An cimma wannan yarjejeniyar haɗin guiwar ce a ziyarar sa gwamnan ya kai Amurka makon jiya, a Washington D.C., tsakanin ƙwararrun masana harkokin noma ma Jigawa da gwamnan ya tafi da su, da kuwa wakilan John Deere da na Tata International.

Tattaunawar ta su ta maida hankali wajen bunƙasa noman zamani, zaburar da matasa su rungumi harkokin noma wurjanjan, sai kuma hanyoyin bunƙasa rayuwar manoma a faɗin Jihar Jigawa.

Daga cikin yarjejeniyar da aka cimma akwai bijiro da bunƙasa noma ta hanyar cinikin taraktocin noma guda 300 daga kamfanin John Deere, waɗanda har an shirya aikawa da su Jihar Jigawa nan ba da daɗewa ba.

Wannan shiri zai ƙara sauƙaƙa hanyoyin hanyoyin bunƙasa noma a rukunin ƙananan manoma.

Wannan shiri an tsara zai samar wa matasa 1,200 dabarun gogewa da aikin noma ta hanyar karɓar haya, bada haya da kulawa da manyan motoci ko kayan aikin noma da kuma gyaran su.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Namadi, Hamisu Gumel ya fitar, ya ce babban abin da ake son a cimma a wajen matasan shi ne faɗaɗa masu ilmi da fahimtar dabarun noma a sauƙaƙe, ya hanyar ci gaba da jan hankalin matasa fantsama cikin harkokin noma, kasancewa hakan ne zai jaddada wadatar abinci a faɗin Jihar Jigawa.

Ta hanyar wannan shiri, Gwamnatin Namadi ta na so ta ƙirƙiro hanyoyin bunƙasa dabarun noma, kamar yadda tsarin yake a cikin ajandoji 12 na gwamnatin sa.

Gwamna Namadi ya bayyana muhimmancin rungumar dabarun bunƙasa harkokin noma na zamani, wato fasaha da zaburas da matasa samun hanya madogara domin samun tagomashi a harkokin noma a jihar.

Gwamna Namadi ya ce ta hanyar haɗin gwiwa da John Deere da kuma babban dilan su Tata International, Jihar Jigawa ta kamo hanyar gina gagarimin shirin bunƙasa harkokin noma na zamani, wanda zai bunƙasa yankunan jihar a fannin noma, wanda shi ne tushen arzikin yankunan karkara.

People are also reading