Za a Dakatar da Manchester United Daga Buga Gasar Europa? INEOS Ya Yi Magana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Akwai shakku kan halartar Manchester United a gasar cin kofin Europa a kakar wasa mai zuwa, duk da nasarar da ta yi a gasar cin kofin FA a karawarta da Manchester City.
Nasarar da ta samu da ci 2-1 a filin wasa na Wembley, na nufin cewa tawagar Erik ten Hag za su buga gasar tare da Tottenham Hotspur.
To sai dai kuma, kamfanin INEOS da ya mallaki Man United shi ne ya mallaki kungiyar Nice da ke Faransa, abin da ya sabawa dokar busa Europa, in ji rahoton Goal.com.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar Nice ta Faransa da Man United, wadanda ke karkashin ikon shugaban kamfanin INEOS, Sir Jim Ratcliffe, sun samu shiga gasar cin kofin Europa na kakar wasa mai zuwa.
Sai dai wata takardar dokoki na hukumar UEFA ta bayyana cewa kungiyoyin da suke karkashin ikon mutum daya ba za su iya shiga gasar Europa ba.
Kafar labaran Daily Mail ta ruwaito kamfanin INEOS ya fitar da sanarwa da ke cewa:
"Muna sane da matsayin kungiyoyin biyu kuma muna tattaunawa kai tsaye da UEFA.
"Muna da yakinin cewa za mu samu mafita gabanin fara gasar Europa a kakar wasa mai zuwa."
A cewar rahoton The Sun, an cimma yarjejeniya da UEFA game da matsayin United da kuma Nice a gasar cin kofin Europa.
Wani shirin farko da INEOS ya so yi ya shafi kara yawan hannun jari zuwasama da kaso 30, wanda hakan ke nufin cewa kungiyar United ce za ta keta dokokin UEFA.
A halin yanzu dai ko da kamfanin ya samu damar tsallake wannan matakin na yawan hannayen jari, ɗaya daga cikin kungiyoyin biyu ba zai buga gasar ta Europa.
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta yi hannun riga da mai horar da 'yan wasanta, Xavi Hernández.
Xavi, wanda ya buga wa Barça wasanni sama da 700 a matsayin dan wasa, ya karbi ragamar horar da kungiyar a shekarar 2021.
Asali: Legit.ng