Rundunar 'yan Sanda ta Dakume Wadanda Ake Zargi ga Kawo Tarnaki a Tsaron Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta bayyana samun nasara kan wasu miyagu da ke taimakawa ‘yan ta’adda su na muzgunawa al’umaar kasar nan a babban birnin tarayya Abuja.
Rundunar ta kama matasa shida da ta bayyana sunayensu da Ndubuisi Okeh, John Jock, Nafiu Tijani, Nasiru Sulaiman, John Njoku, da Suleiman Musa a wani samame da ACP Mohammed S. Baba ya jagoranta.
Vanguard News ta tattaro cewa ana zargin matasan da rashin kishin kasa inda su ke sayarwa ‘yan ta’adda layukan waya da aka riga aka yi wa rajista .
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kwato layukan waya masu rajista 1,100 daga hannun wasu matasa shida da ake zargi da sayarwa ‘yan ta’adda layukan ba bisa ka'aida ba.
A wata tattaunawa da manema labarai, kwamishinan ‘yan sandan Abuja CP Benneth Igweh ya ce suna sayar da layukan a kan N3000 zuwa N5000 ga miyagun.
Ya ce wannan danyen aiki na kawo babban cikas wajen yaki da ta’addanci da jami’an tsaro ke yi, kuma ya nuna karara cewa akwai matsala a sashen sadarwar kasar nan, kamar yadda Politics Nigeria ta wallafa.
A Karin nasarori da su ka samu, CP Igweh ya ce jami’ansu sun yi ram da ‘yan fashi da makami, masu safarar makamai, barayin motoci da masu garkuwa da mutane.
A baya mun kawo muku labarin cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta fattaaki sansanin wasu bata gari a babban birnin tarayya Abuja tare da cafke miyagu hudu.
Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, Josephine Adeh ta fitar ta ce wadanda aka kama sun hada da Yahaya Abubakar mazaunin Mpape, Mohammed Mohammed, Umar Aliyu da Nura Abdullahi.
Asali: Legit.ng