Home Back

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Tare Fasinjoji a Yobe, Sun Hallaka Mutum 3

legit.ng 2024/7/3
  • Ƴan ta'addan Boko Haram sun tare fasinjoji suna tsaka da tafiya a kan hanyar Biu zuwa Damaturu a jihar Yobe
  • Miyagun waɗanda suka ɗauki mutum huɗu daga cikin fasinjojin, sun hallaka mutum uku daga cikinsu bayan sun kai su zuwa cikin daji
  • Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta yi kira ga gwamnati da jami'an tsaro da su ƙara zage damtse domin kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta'adda

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kashe fasinjoji uku da ke kan titin hanyar Biu zuwa Damaturu a jihar Yobe.

Maharan sun yi awon gaba da su ne a kan hanyar a ranar Laraba kafin daga bisani su kashe su.

Yan ta'adda Boko Haram sun hallaka mutane a Yobe
'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka mutum uku a Yobe Asali: Original

Yadda ƴan ta'adda suka kai harin

Tashar Channels tv ta ce wani ɗan uwan ɗaya daga cikin mutanen da harin ya ritsa da su, ya ce lamarin ya faru ne a kusa da garin Kamuya, dake kan iyakar Yobe da Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa mutum uku ne daga cikin fasinjojin waɗanda Kiristoci ne aka sace yayin da aka ƙyale sauran.

"Suna taho ne daga Biu, kwatsam sai maharan suka tsayar da motarsu, sannan suka tafi da mutum huɗu waɗanda Kiristoci ne zuwa cikin daji inda suka kashe uku daga cikinsu. Daga baya mun ga gawarwakinsu a shafukan sada zumunta."
"Mun ga gawarwaki uku ne kawai daga cikin mutum hudun da aka sace. Ba mu san inda ɗayan yake ba."

- Wata majiya

CAN ta yi kira ga gwamnati

Sakataren ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Rabaran Ibrahim Abako yayi Allah wadai da faruwar lamarin.

Ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su ƙara zage damtse a ƙoƙarin da suke yi na yaƙar masu tada ƙayar baya.

"A madadin ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Yobe, mun yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa matasa Kiristoci a hanyar Damaturu zuwa Biu.”
"Wannan lamarin yana faruwa akai-akai. Muna kira ga gwamnati musamman sojoji da ƴan sanda da su ɗauki matakan da suka dace ta hanyar kare fararen hula ba tare da la’akari da addininsu ba."

- Rabaran Ibrahim Abako

Ƴan ta'adda sun kashe DPO

A wani labarin kuma, kun ji cewa Wasu da ake zargin ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP ne sun kashe wani babban jami'in ƴan sanda a yankin Arewacin jihar Borno.

Ƴan ta'addan na ISWAP sun kutsa cikin Sabuwar Marte da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Litinin inda suka far wa wani ma’aikacin lafiya wanda ya yi sa’a ya tsere.

Asali: Legit.ng

People are also reading