Home Back

Magana Ta Ƙare, Bankin Duniya Ya Ba Najeriya Bashin $2.2bn, Ministan Tinubu Ya Magantu

legit.ng 2024/7/3
  • Bankin Duniya ya amince ya ba Najeriya jimillar bashin $2.25bn domin sake fasali da daidaita tattalin arzikin kasar
  • Wannan bashin na $2.25bn zai taimakawa kokarin Najeriya na dawo da tattalin arziki da tallafawa talakawan kasar
  • A cewar ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun tallafin bankin duniyan zai taimaka wajen aiwatar da kasafin kudi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bankin Duniya ya amince ya ba Najeriya basussuka guda biyu: $1.5bn domin sake fasali da daidaita tattalin arzikin Najeriya (RESET) da nufin aiwatar da tsare-tsaren gwamnati (DPF).

Bankin Duniyan ya kuma amince da ba Najeriya bashin $750m domin sauya fasalin hanyoyin samar da kayan aiki na Najeriya (ARMOR) da nufin aiwatar da 'shiri domin sakamako' (PforR).

Bankin Duniya ya ba Najeriya bashin $2.2bn
Bankin Duniya ya amince da bukatar Tinubu na ba Najeriya bashin $2.2bn. Hoto: @officialABAT, @WorldBank Asali: Facebook

Bankin Duniya ya ba Najeriya bashin $2.25bn

Wannan bashin na $2.25bn zai taimakawa kokarin Najeriya na daidaita tattalin arziki da tallafawa talakawa da masu fama da matsalar tattalin arziki, in ji rahoton bankin duniyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan bashin zai kuma kara tallafawa kokarin Najeriya na tara kudaden shiga ba na man fetur ba da kuma kare kudaden shigar man domin tabbatar da dorewar kasafin kudi.

Yayin da Najeriya ke fuskantar matsalar tattalin arziki mai, ta fahimci bukatar fara sauye-sauye masu mahimmanci domin inganta tattalin arziki da karfafa kasafin kudi.

Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan bashin

Jaridar The Cable ta ruwaito ministan kudi kuma ministan tattalin arziki, Wale Edun, ya ba da sanarwar amincewar Bankin Duniya na ba Najeriya bashin $2.25bn.

A cewar wata sanarwa a ranar Alhamis, Wale Edun ya ce wannan wani bangare ne na kokarin da Shugaba Bola Tinubu yake yi na daidaita tattalin arzikin kasar.

Sanarwar ta samu sa hannun Mohammed Manga daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar kudi da kuma tattalin arziki.

Da yake tsokaci kan wannan bashi, Edun ya yi maraba da tallafin da bankin duniya ke ba Najeriya.

Katsina: An tallafawa iyalan jami'an tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya bada tallafin Naira miliyan shida ga iyalan jami'an tsaro da aka kashe a makon jiya.

Kowanne iyali na 'yan sandan ya samu N500,000 yayin da aka bada tallafin N1,000,000 ga kowanne iyali na jami'an tsaron jihar guda uku.

Asali: Legit.ng

People are also reading