Home Back

Tsadar Man Fetur ya Jefa Manoman Shinkafa a Jigawa Cikin Masifa: Wa zai kawo musu Dauki? Daga Ahmed Ilallah

premiumtimesng.com 2024/5/17
TANTANCE MA’AIKATAN JIHAR JIGAWA NA SHIRIN BARIN BAYA DA KURA: Tsokaci ga Maigirma Gwamna, Daga Ahmed Ilallah

Yau ranar ma’aikata ce, mu tuna cewa ba kawai ma’aikatan gwamnati ko manyan masana’antu ne kadai ma’aikata ba.

Noma ne yake samar da aikin yi sama da kashi hamsin na aiyukan yi a Nijeriya, sannan ita ce sana’ar mafi girman da al’ummah suka dogara da ita.

Kalubalen da harkar noma ya ke fuskanta ne, ya Sanya kasar da ta fada cikin masifar talauci, yunwa da ma rashin zaman lafiya.

Jahar Jigawa dake kan gaba a wajen noma, musamman ma noman Shinkafa.

Amma a kusan kowace shekara manoman kan fuskaci kalubale kala kala, wanda kan jawo musa asara lokaci zuwa lokaci, dewa ma su kan hakura da noman.

A bana ma, da a ke fama da tsananin zafi, sakamakon chanjin yanayi, shuka na bukatar ban ruwa a kan kari, sai ga wata sabuwa na karanci da tsadar Man Fetur.

Kusan kashi saba’in koma fiye da haka, sun dogara ne da amfani da injinan bayi da ke amfani da Man Fetur domin ban ruwa a gonakan su.

A wannan lokaci da a ke sayar da Man Fetur din a akasarin jahar Jigawa har sama da dubu Daya a kan Lita guda ta Man Fetur din.

Wannan tsadar Man Fetur din dama karancin sa, ba karamin bala’i bane ga wannan manoman.

Dama da kyar da karfin hali manoman ke noma a wannan kaka, ganin yadda a kasha kashi a noman alkama, ga kuma yanayin da a ke ciki na tsananin talauci da a ke fama da shi.

A wannan hali da a ke ciki, manoman na cikin tsananin tahin hankali a lokacin da amfani ya ke tsakiyar san kulawa da ban ruwa.

Sai gashi Man Fetur ya shiga wani yanayi na tsananin tsada, wanda a yankin Jigawa Masogabas a kan sai da litar Man har sama da dubu daya.

Magana ta gaskiya, in har da gaske a ke a wannan kasa wajen bunkasa noma a wannan jaha da kasa, ya zama dole a duba wannan lamarin.

Ya zama dole a samu hanyar da za a taimakawa wannan manoman domin samo hanyar da za a taimakawa wannan manoman.

People are also reading