Home Back

Ce-ce-kuce ya barke kan batun rage wa mai alfarma Sarkin Musulmi karfin iko

bbc.com 2024/7/3
Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Asalin hoton, DAULAR USMANIYYA

A Najeriya, batun tattaunawa a kan dokar da ta shafi rage wa mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku, karfin iko da majalisar dokokin jihar Sokoto zata yi ya janyo ce-ce-kuce.

‘Yan majalisar zartaswa jihar ta Sokoto ne dai suka gabatar da kudurin dokar da ta shafi rage wa mai alfarma Sarkin Musulmin karfin iko.

Wannan sabuwar tika-tirka dai na ci gaba da jan hankalin al’ummar Najeriya da ma makwabtan kasar bisa la’akari da irin matsayin da sarautar Sarkin Musulmi dama Daular Usmaniyya ta ke a idon duniya.

Yunkurin da ‘yan majalisar zartaswar jihar Sokoto suka na gabatar da kudurin dokar da zai yi kwaskwarima ga tsarin gudanarwar majalisar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya hada da yin sauye-sauyen da za su kai ga rage masa karfin iko ta kowanne bangare.

Kudurin dokar dai ya kunshi dakatar da mai alfarma Sarkin Musulmin daga nada ko cire hakimi ko dagaci ko kuma kowacce irin sarautar gargajiya a jihar abin da ke nuni da cewa ya zama sarki marar iko a jihar.

Tuni dai mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima, ya bayyana matakin majalisar zartaswar a maysayin kuskure.

“ Ya ce mai alfarma Sarkin Musulmi, shi ne wanda za a ambata da tabbataccen tambari na magance dukkan matsalolin da ke kawo tarnaki ga ci gaban Najeriya.”

Ya ce, “Ya kamata majalisar zartaswa ta Sokoto ta sani cewa ko shakka babu mai alfarma Sarkin Musulmi shi ne sarkin da aka sani a matsayin zabin jama’a, kuma masarautarsa ya zama dole a martabata gami da daukakata domin ci gaban kasarmu.” In ji mataimakin shugaban Najeriyar.

Shi ma daya daga cikin ‘ya’yan masarautar Bada a jihar Kebbi, Farfesa Bello Daudan Bada, ya shaida wa BBC cewa Daular Usmaniyya na da matukar muhimmanci, inda ya yi kira ga gwamnatin jihar ta Sokoto da ta sake nazari a kan kudurin dokar da majalisar zartaswar ta gabatar.

Ya ce,” Masarauta ita ce wadda mutane suka gada kuma ta gad esu, tana da nata tasirin, wannan abu ne da sai an samu hadin kai tsakanin su shugabannin da aka zaba na siyasa da kuma masarauta, don idan har gwamnati na neman hadin kan sarakuna ba wuya ta same shi, don haka hadin kan shi ne maslaha ga kowa.”

Wannan tirka-tirka dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da a jihar Kano ma ake tsaka da jayayya kan sarautar Sarkin Kanon, bayan da gwamnatin jihar ta yi sauye-sauye a dokar masarautu abin da ya janyo cire Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, tare da dawo da Muhammadu Sanusi na II kan mulkin.

People are also reading