Home Back

TA FARU TA ƘARE: El-Rufai ya tafka harkalla da kuɗaden Kaduna – Majalisar Kaduna

premiumtimesng.com 2024/7/3
GOGUWAR PDP A AREWA: APCn El-Rufai ta sha kasa, Atiku ya lashe zaɓen shugaban kasa a Kaduna da ratan kuri’u sama da 150,000

Majalisar jihar Kaduna ta shawarci gwamnan jihar Uba Sani da ya taso keyar tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai, ya yi bayani filla-filla yadda ya kashe miliyoyin dalolin da ya ciyo bashi lokacin yana mulkin jihar.

Idan ba a manta ba watannin biyu da suka wuce majalisar jihar ta kafa wata kwamiti domin ta binciki yadda aka kashe kuɗaɗen da gwamna Nasir El-Rufai ya ciyo bashi daga kasashen waje ya kashe su da sunan yin aiki a jihar.

Majalisar na zargin El-Rufai da karya dokokin ƙasa ta hanyar karɓo basussuka ba bisa ƙa’ida ba, da kuma harƙallar karkatar da maƙudan kuɗaɗe.

El-Rufai ya yi gwamna daga 2015 zuwa 2023, kuma shi ya ɗaure wa Gwamna Uba Sani gindi har ya samu nasarar hawa mulki a zaɓen 2023.

‘Yan Majalisar Kaduna sun ce sun ɗauki wannan mataki ne bayan kwamitin bincike da majalisar ta kafa ya gabatar da rahoton sa, ƙarƙashin shugaban kwamitin, Honorabul Henry Zacharia.

Zacharia ya gabatar da rahoton sa a ranar Laraba, yayin zaman majalisa.

Ya rohoton ya ragargaji gwamnatin El-Rufai, musamman kan bauɗaɗɗun hanyoyin da kwamitin ya ce El-Rufai ya bi ya karɓo basussuka na biliyoyin nairori, ba bisa ƙa’ida ba.

Rahoton ya yi zargin cewa bashin da El-Rufai ya karɓo ba a yi aiki da kuɗaɗen ta yadda ta dace ba, a wasu basussukan ma ba a bi ƙa’ida wajen ciwo su ba.

“Saboda haka kwamitin ya nemi a gurfanar da El-Rufai bayan jami’an hana cin hanci da rashawa sun bincike shi, tare da wasu kwamishinonin sa, bisa zargin yin ɓaranƙyanƙyamar kwangiloli, karkatar da maƙudan kuɗaɗen al’ummar Jihar Kaduna da kuma aikata zambar harƙallar kuɗaɗe.” Haka dai rahoton ya bayyana.

People are also reading