Home Back

Shin me ya sa ƙasashen yammaci ke shakkar manhajar Tiktok?

bbc.com 2024/5/19
tiktok user

Asalin hoton, AFP

kasar China ta soki wani kuduri da 'yan majalisar Amurka ke yi wa karatu wanda kuma zai iya kai wa ga haramta amfani da kafar Tiktok a Amurkar, wani abu da Chinar ta bayyana da rashin adalci.

Wannan ne dai mataki na baya-bayan a shekarun da kasashen biyu suka kwashe suna zaman tankiya dangane da fargaba kan manhajar wadda wani kamfanin kasar China ya mallaka.

Kasashen yammaci da dama dai sun haramtawa jami'ai da 'yan siyasa da jami'an tsaro sauko da manhajar ta Tiktok a na'u'rorin gwamnatocinsu.

Shin wadanne dalilai ne ke sa ake shakkar wannan manhaja ta Tiktok? Sannan ta yaya kamfanin ke magance su?. Ga wasu dalilai guda uku.

1. TikTok na karɓar bayanai masu yawa daga abokan hulda

TikTok ya ce tsarin karbar bayanai na manhajar na gudana ne bisa yadda ake yi a duniya fasahar sadarwa.

Masu suka na yawaita sukar Tiktok da tara bayanai masu yawa. Wani rahoton tsaro na intanet da wasu masu bincike na kamfanin Internet 2.0 na kasar Australia suka wallafa a watan Yulin 2022 yana zama madogara.

Masu binciken sun yi nazarin yadda manhajar ke tattara bayanai kuma sun ce tana "tattara bayanai masu yawa".

Masana sun ce Tiktok yana tattara bayanai da suka hada da wurin da mutum yake da irin wayar da mutum ke amfani da ita da kuma sauran manhajojin da ke kan wayar.

To sai dai a wani gwaji irin wannan da kamfanin Citizen Lab ya gudanar ' idan aka kwatanta da yadda wasu kafafen sada zumunta, Tiktok na karbar bayanai masu alaka da yadda za a iya bibiyar abokin hulda.

Harwayau, wani rahoto da cibiyar fasahar sadarwa ta Georgia ta fitar a bara ya ce "gaskiyar dai ita ce mafi yawancin kafafen sadarwa da manhajojin wayoyin hannu abu iri guda suke yi."

2. Akwai yiwuwar gwamnatin China ka iya amfani da TikTok wajen leken asirin masu amfani da manhajar

TikTok ya ce kamfanin yana da cikakken 'yanci kuma "bai taba bai wa gwamnatin China bayanan masu hulda da shi ba kuma ba za su bayar ba ko da ta tambaye mu."

Duk da cewa dai al'amarin na ci wa kwararru tuwo a kwarya, mafi yawancinmu mun yadda cewa mika dumbin bayanai ga kafofin sada zumunci da muke mu'amila da su shi ne abin da muke yi.

Su kuma suna tattara bayananmu su yi amfani da shi wajen tallata hajoji a shafukansu, ko kuma su sayar da bayan namu ga wasu kamfanoni da ke son tallata mata hajarsu a intanet.

Matsalar da masu sukar Tiktok ke da ita da kamfanin ita ce kasancewarsa mallakar babban kamfanin kasar Chinan ne, ByteDance, wani abun da ya fitar da manhajar zakkar cewa ba mallakin Amurkawa ba ne.

Misali Facebook da Snapchat da Instagram da kuma Youtube dukkan su na karbar bayanai irin na Tiktok to amma su din mallakar kamfanonin Amurka ne.

Asalin hoton, Getty Images

bytedance headquarters
Bayanan hoto, Kamfanin ByteDance ne yake da mallakin TikTok

Shekaru da dama ƴan majalisar dokokin Amurka, tare da yawancin sauran ƙasashen duniya, sun ɗauki matakin amincewa: cewa ba za a yi amfani da bayanan da waɗannan shafuka suka tattara ba saboda dalilan da ka iya jefa tsaron ƙasa cikin haɗari.

Umurnin zartarwa na Donald Trump na shekara ta 2020 ya yi zargin tattara bayanan TikTok na iya baiwa China damar bibiyar wuraren ma'aikatan tarayya da ƴan kwangila da samun bayanan sirri don yaudara, da kuma yin leƙen asiri na kamfanoni".

Mataki na bakwai a dokar leken asiri ta kasar Chaina ya bayyana cewa, ya kamata dukkan kungiyoyi da 'yan kasar Chaina su ba da goyon baya da taimako a fannin ayyukan leken asirin kasar.

Ana bayar da misali da yadda mutane suke zargin kamfanonin Chaina ba Tik Tok ba kawai.

A shekara ta 2020, shugabannin TikTok sun sake tabbatar wa mutane cewa jami'an Chaina ba za su sami damar yiwa wadanda ba ƴan kasar ba kutse.

Amma a cikin shekara ta 2022, ByteDance ya yarda cewa da yawa daga cikin ma'aikatanta na Beijing sun sami damar yin amfani da bayanan aƙalla 'yan jarida biyu a Amurka da Burtaniya don bin diddigin wurarensu tare da bincika ko suna saduwa da ma'aikatan TikTok waɗanda ake zargi da watsa bayanai ga kafofin labarai.

Mai magana da yawun TikTok ta ce tuni aka sallami ma'aikatan da suka yi kutsen daga aiki.

3. Ana iya amfani da TikTok don sauya tunani

TikTok ya ba da hujjar cewa ya haramta bayanan da za su iya cutar da al'ummar.

A cikin watan Nuwamban shekara ta 2022, Christopher Wray babban jami'i a Ofishin hukumar tsaro ta FBI ya shaidawa 'yan majalisar dokokin Amurka: "Gwamnatin Chaina za ta iya amfani da wannan dama wajen cin bayanan sirri.

Wadannan damuwar sun kara fusata da gaskiyar cewa 'yar'uwar TikTok, Douyin - wacce ke akwai kawai a cikin Sin - ana yin sharhi sosai kuma an ba da rahoton ƙirƙira don ƙarfafa kayan ilimi da inganci don yin hoto ko bidiyo mai zagaya yanar gizo da sauri.

An tsoratar game da yadda takwarar Tiktok, Douyin wadda ake amfani da ita a China ake amfani da ita wajen koyar da ilimi duk da cewar hukuma na tace ayyukanta.

Ana sanyawa dukkan shafukan sada zumunta ido a Chaina, yan sanda nagoge duk wani abu da ya soki gwamnati ho kuma ya tayar da tarzoma.

Da farko TikTok, na tantance manyna laifuka a manhaar: wata mai amfani da tiktok daga Amurka ta bayyana yadda aka dakatar da shafinta saboda ta tattauna da mabiyanta game da yadda Beijing ta ke mu'amala da mabiya Addinin Islama . Bayan mummunan martani da jama'a suka yi TikTok ya nemi afuwa tare da dawo da shafinta

douyin app

Asalin hoton, Getty Images

Masu binciken a shekara ta 2021, sun bayyana cewar dandalin ba ya fidda bayanan bayan fage.

Manazarta Cibiyar Fasaha ta Georgia sun kuma yi bincike kan batutuwa irin su 'yancin kai a Taiwan ko kuma yiwa firaiministan Chaina, nda suka kammala da cewa: "Ana iya samun faifan bidiyo a cikin dukkan wadannan nau'o'in a TikTok cikin sauki. Yawancinsu sun shahara kuma ana yaɗa su a ko'ina.

Hatsarin ƙa'idar

An riga an dakatar da manhajar a Indiya, wadda ta ɗauki mataki a shekara ta 2020 da sauran dandalin sada zumunta da dama na Chaina.

Amma haramcin Amurka kan TikTok na iya yin tasiri sosai a kan dandalin, tunda galibi ƙawayen Amurka sun goyi bayan matakin.

People are also reading