Kashim Shettima Ya Bayyana Yadda Tinubu Ya Gina Atiku da Sauran Mutane a Siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ya siffanta shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin gwarzon dimokuraɗiyya a Najeriya.
Sanata Kashim Shettima ya faɗi haka ne ganin yadda shugaban kasar ya dauki shekaru yana taimakon yan siyasa a kasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasar ya yi jawabin ne a lokacin wani taro da aka shirya domin murnar ranar dimokuraɗiyya a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa ba za a taɓa mantawa da Bola Tinubu ba a tarihin jam'iyyun adawa a Najeriya.
Shettima ya ce a Bola Tinubu ya zama bango ne da dukkan ƴan adawa ke jingina da shi a lokacin mulkin PDP kuma ya yaki tsarin kafa jam'iyya daya a kasar.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa Bola Tinubu ya gina yan siyasa da dama a dukkan bangarorin Najeriya, rahoton Daily Post.
Cikin manyan yan siyasa da Tinubu ya taimaka Shettima ya ambaci Atiku Abubakar, Olusegun Mimiko, Rauf Aregbesola da Adams Oshimole.
Har ila yau Kashim Shettima ya ce a lokacin da aka kori Atiku Abubakar daga PDP wajen Bola Tinubu yaje neman mafita.
Ya ce a lokacin Bola Tinubu ya karbi Atiku Abubakar hannu biyu biyu har ma ya ba shi damar tsayawa takara a jam'iyyar AC.
A wani rahoton, kun ji cewa Kashim Shettima ya fasa tafiyar da aka tsara zai wakilci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a taron kuwanci a Dallas.
Mataimakin shugaban ƙasar ya soke wannan tafiya ne sakamakon wata tangarɗa da jirginsa ya samu, ministan waje ne ya wakilci Tinubu a taron.
Asali: Legit.ng