"Ku Kuka Jawo": Jigon NNPP Ya Fadi Kuskuren 'Yan Najeriya Wajen Zaben Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana ra’ayinsa kan taɓarɓarewar da tattalin arziƙin ƙasar nan yayi.
Buba Galadima ya bayyana cewa waɗanda suka zaɓi Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023 bai kamata su yi ƙorafi ba.
Ya jaddada cewa ƴan Najeriya sun yi watsi da gargaɗin da ya yi game da zaɓen dan takarar APC, Bola Ahmed Tinubu wanda ya yi nasara a kan Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata hira da ta yi da Saturday Sun, Buba Galadima ya ce an shawarci masu kaɗa ƙuri'a da kada su goyi bayan Tinubu, amma suka yi kunnen uwar shegu.
A kalamansa:
“Ah! Ah! Na ɗauka ku kuka zaɓe shi. Idan aka ce maka kada ka yi kaza, zai ƙona yatsanka, kuma ka je ka yi, laifin wa zaka gani?"
Buba Galadima ya kuma bayyana cewa, Shugaba Tinubu bai yi wani takamaiman alƙawari ga masu zaɓe ba.
Ya buƙaci a nuna masa wata shaida wacce za ta nuna shugaban ƙasan yana yin alƙawarin zai yi aiwatar da wasu manufofi idan ya hau kan mulki.
"Ina so in yi muku tambaya ɗaya. Ko za ka iya nuna min wata takarda da Tinubu ya ce zai yi kaza, zai yi wannan ko zai yi wancan?"
"Za a iya nuna min? Bai yi alƙawarin komai ba. Kuma kuka zaɓe shi. Domin haka ga ku ga shi nan."
- Buba Galadima
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Ondo kuma jigo a jam'iyyar PDP, Cif Bode George ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙarawa shugaban ƙasa Bola Tinubu lokaci.
Bode George ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara shekara ɗaya ga Shugaba Tinubu domin ya cika alƙawuran da ya ɗauka wajen yaƙin neman zaɓe na gyara ƙasar nan.
Asali: Legit.ng