Home Back

Li Qiang Ya Yi Kira Ga Sin Da Equatorial Guinea Da Su Kare Moriyar Bai Daya Ta Kasashe Masu Tasowa

leadership.ng 2024/7/1
Li Qiang Ya Yi Kira Ga Sin Da Equatorial Guinea Da Su Kare Moriyar Bai Daya Ta Kasashe Masu Tasowa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga Sin da Equatorial Guinea, da su yi aiki tare, wajen ingiza matakan kare daidaito da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, su kuma tsaya tsayin daka wajen kare moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa.

Li ya yi kiran ne yau Laraba a zauren taron jama’a dake birnin Beijing, yayin zantawarsa da shugaban kasar Equatorial Guinean Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, wanda ke ziyarar aiki a kasar ta Sin.

Firaministan na Sin, ya ce, sassan biyu sun bayyana daga matsayin alakar kasashensu, zuwa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, kuma Sin ta sha alwashin yin aiki tare da Equatorial Guinea, wajen aiwatar da muhimman kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da yayata kawancen gargajiya, da zurfafa hadin gwiwar cimma moriyar juna, da ci gaba da kyautata zamantakewar al’ummun sassan biyu. (Saminu Alhassan)

People are also reading