Home Back

'Tilastawa mutane su zauna a gida tamkar cin amanar kasa ne'

bbc.com 2024/7/7

Asalin hoton, Presidency

Shugaban Nijeriya
Bayanan hoto, Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhini kan kisan sojojin kasar biyar da ake zargin mayakan haramtacciyar kungiyar nan ta IPOB da hannu a harin da aka kai mu su.

Sojojin da aka kashe suna aikin wanzar da zaman lafiya ne a garin Aba da ke jihar Abia a ranar Alhamis kuma al'amarin ne na zuwa ne bayan watanni biyu kacal da faruwar wani mummunan al’amari a garin Okuama da ke jihar Delta.

A cikin sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar, shugaba Tinubu ya yi ‘Alla-wadai da wadannan munanan ayyuika na dabbanci'kuma bai kamata a kyale su a cikin kasarmu ba’.

‘’ Sojojinmu da ‘yan sanda suna da hakkin kare dukkanmu daga ‘yan ta’ada da kuma mahara. Daruruwansu sun rasa rayukansu wajan sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, yayin da wasu kuma suka gamu da wulakanci daga hannun mutanen da suke karewa’’, in ji shi.

Shugaba Tinubu ya sha alwashin gwamnatinsa za ta dauki matakin dakile ayuikan wadanda suka maida hankalin wajan kai hari ba gaira ba dalili akan dakarun kasar.

‘’Ina son na bayyana cewa gwamnatin tarraya da sojojin kasar suna da karfin murkushe masu tayar da kayar baya, wandanda ke janyo wa al’ummominsu rashin tsaro’’

‘’Ina kira ga jami’an tsaro da su kama wadanda suke da hannu a cikin al’amarin da masu kiran mutane su zauna a gida. Wannan mataki ba komai bane illa cin amanar kasa'' in ji shi.

Shugaba Tinubun ya mika ta’aziyya ga iyalan sojojin biyar da aka kashe tare da yin kira ga takwarorinsu a kan kada su yi kasa a gwiwa wajan gudanar da ayuikan wanzar da lafiya sakamakon harin da ya faru a garin Aba.

Rundunar sojin Najeriya ita ma ta yi Alla wadai da al’amarin kuma ta sha lashi takobin hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.

People are also reading