Home Back

'Yan Bindiga Sun Buɗe Wuta, Sun Kashe Kansila da Shugaban Kungiyar Matasa

legit.ng 2024/7/1

Ebonyi - Wasu miyagun ƴan bindiga sun hallaka mutum biyu, Stanley Akpa Nweze and Arinze Joshua Ugochukwu a kauyen Isu da ke ƙaramar hukumar Onitch a Ebonyi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ɗaya daga cikin waɗanda maharan suka kashe, Mista Nweze shi ne kansila mai wakiltar gundumar Enuagu a majalisar ƙaramar hukumar Onitcha.

Ɗayan mutumin da aka kashe a harin, Arinze Joshua Ugochukwu, ya kasance kodinetan ƙungiyar matasan Najeriya (NYCN) reshen Onitcha a jihar Ebonyi.

The Nation ta rahoto cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai wa Stanley da Arinze hari tare da kashe su a ranar Litinin a yankin Amanator da ke ƙauyen Isu.

Wasu majiyoyi daga yankin sun shaida cewa matasan biyu na kan babur suna tafiya zasu dawo Isu lokacin da ƴan bindigar suka tare su.

Maharan sun buɗe masu wuta nan take, sai da suka tabbatar duk sun mutu sannan suka bar wurin, in ji majiyoyi.

Haka nan kuma ƴan bindigar sun ci gaɓa da harbin isa domin tsorata masu wucewa kafin daga bisani suka tsere zuwa cikin daji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku saurari ƙarin bayani...

Asali: Legit.ng

People are also reading