Home Back

Ba za mu kyale ƴan Najeriya su riƙa watangaririya a Makka bayan Hajji ba, da an kammala za dawo gida – Arabi

premiumtimesng.com 2024/7/4
Ba za mu kyale ƴan Najeriya su riƙa watangaririya a Makka bayan Hajji ba, da an kammala za dawo gida – Arabi

Shugaban Hukumar Alhazai Jalal Arabi ya bayyana cewa bana Alhazan Najeriya vza su dawo gida da an kammala aikin Haji.

Arabi ya faɗi haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a filin jirgin sama na Madina lokacin da jirgin Karshe daga Najeriya ta sauka a Madina.

Arabi ya ce wannan shine karo na farko cikin shekaru da dama Najeriya ta kammala aikin jigilar Alhazai awa 72 kafin a rufe filin jirgin saman Saudi Arabiya.

” Muna ma Allah godiya bisa wannnan nasara da muka samu, muna cuke da farin ciki matuka fanin cewa ana fara wannan aiki lafiya gashi kuma mun kammala shi lafiya cikin Ikon Allah.

” Ba wayon mu ba ne ko dabarar mu, Allah ne ya sa mana hannu kuma muna godiya masa matuka. Sannan kuma ina mai yi wa ƴan Najeriya albishir da zarar an kammala aikin Hajji, za a fara jigilar Alhazai zuwa gida.

” Ba za mu bari alhazan mu su riƙa watangaririya a garin Makka ba, alhali alhazan wasu kasashen sun koma gida ba. Muma namu daga an kammala aikin Hajji za mu kwashe zuwa Najeriya, kowa ya je ta ga iyali.

Akalla mahajjata sama sa 50,000 ne hukumar NAHCON ta yi jigilar su zuwa kasa mai tsarki daga Najeriya.

Sannan kuma akwai wasu mutum 12,000 da suka zo aikin Hajji ta jirgin yawo daga Najeriya suma.

Mahajjata dai za su ɗunguma zuwa Arafat ranar Asabar, inda za a gudanar da sallar Eid El Kabir Ranar Asabar.

People are also reading