Home Back

Ba Mu Janye Yajin Aiki Ba – NLC

leadership.ng 2024/6/29
Ba Mu Janye Yajin Aiki Ba – NLC

Kungiyar kwadago (NLC), ta bayyana cewa har yanzu ba ta janye yajin aikin da ta fara ba duk da tattaunawar da ta ke yi da gwamnatin tarayya.

NLC ta bayyana haka ne a shafinta na X (Twitter) a ranar Talata.

“Muna ci gaba da yajin aiki har sai mun ji daga shugabancinmu a tattaunawar da aka shirya yi a yau 4 ga watan Yuni.”

A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyoyin kwadagon NLC da TUC a wani taron gaggawa da ta gudanar.

Ganawar karkashin jagorancin sakataren gwamnatin kasar, George Akume a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin sai abin da hali ya yi da kungiyoyin kwadagon suka fara.

Bangarorin biyu sun shafe sa’oi biyar zuwa shidda suna tattaunawa da juna kuma a karshe sun cimma matsaya a kan wasu batutuwa.

Yajin aikin na kungiyoyin kwadagon ya tsayar da harkokin yau kullum da suka hadar da aikin gwamnati, asibitoci, sufurin jiragen sama da sauransu a Nijeriya.

People are also reading