Home Back

MDD Ta Amince Da Kudirin Sin Na Kafa Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kai Na Duniya

leadership.ng 2024/7/5
MDD Ta Amince Da Kudirin Sin Na Kafa Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kai Na Duniya

A ranar Juma’a ne babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 ko UNGA a takaice, ya amince da kudirin da kasar Sin ta gabatar na kafa ranar tattaunawa tsakanin wayewar kai na duniya.

Kudirin ya bayyana cewa, duk nasarorin da aka samu game da wayewar kai, gajiyar bil’Adama ne baki daya. Kudirin ya kuma yi kira da a mutunta mabambantan wayewar kai, yayin da aka mai da hankali kan muhimmiyar rawar da tattaunawar za ta taka wajen wanzar da zaman lafiya a duniya, da inganta ci gaba tare, da kara kawo wa dan Adam alheri, da samun ci gaba tare. Kudirin ya bukaci a yi tattaunawa tsakanin mabambantan wayewar kai cikin adalci da kuma mutunta juna, hakan da ya nuna muhimmin jigon shawarar wayewar kan duniya. Babban taron ya kuma yanke shawarar sanya ranar 10 ga watan Yuni a matsayin ranar tattaunawa tsakanin wayewar kai na duniya. (Yahaya)

People are also reading