Home Back

Wilcox zai yanke shawara kan Ten Hag, Ƙungiyoyi na gogayya kan Oliseh

bbc.com 2024/5/6
Erik ten Hag

Asalin hoton, Getty Images

Sabon darektan Manchester United, Jason Wilcox, zai yi nazari a kan kwarewar Erik ten Hag, kafin kungiyar ta yanke shawara a kan makomar kociyan, dan Holland. (Telegraph)

Kociyan Brighton Roberto de Zerbi shi ne kan gaba a cikin wadanda za a zaba domin maye gurbin Ten Hag idan ya bar Old Trafford, kuma Brighton din na tunanin daukar kociyan Burnley, Vincent Kompany don maye gurbinsa. (Teamtalk)

West Ham za ta tattauna da kociyan Sporting Lisbon Ruben Amorim, yayin da kungiyar ke nazari kan ko za ta tsawaita kwantiragin David Moyes a bazaran nan. (The Athletic )

Tsohon kociyan Wolves Julen Lopetegui na gaba-gaba wajen zama wanda zai iya maye gurbin Moyes a kungiyar ta London. (Telegraph)

Har yanzu Amorim shi ne na daya da Liverpool ta sa a gaba domin maye gurbin Jurgen Klopp to amma kociyan Brentford Thomas Frank ka iya samun aikin idan Amorim, dan Portugal ya tafi wata kungiyar. (Teamtalk)

Haka kuma Bayern Munich ma na tattaunawa kan De Zerbi, ganin cewa wanda suka fi so ya zama kociyansu wato Julian Nagelsmann na neman tawaita kwantiraginsa na tawagar Jamus. (HITC)

Har yanzu kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya na son sayen Kevin de Bruyne na Manchester City a bazara, kuma ana sa ran nan da dan lokaci za ta tuntubi dan wasan na tsakiya dan Belgium, mai shekara 32. (Rudy Galetti)

Barcelona ta bi sahun Arsenal wajen son sayen dan wasan Newcastle United da aka yi masa kudi fam miliyan 90, Alexander Isak, dan Sweden, kuma Barca na sa ran cinikin ya tabbata. (Sun)

Arsenal da Manchester United sun bi sahun kungiyoyin da ke son Micheal Olise na Crystal Palace da Faransa amma kuma suna fuskantar gogayya daga Chelsea, da Manchester City da kuma Juventus. (Football Insider)

Ana sa ran Arsenal ta yi karin manyan 'yan wasa uku ko hudu a bazaran nan, a garambawul din da kungiyar, za ta yi indadan wasan gaba na Sporting Lisbon da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 25, ke ci gaba da zama na daya ta fi son saye. (Football Transfers)

Liverpool ta kalli wasan Gyokeres a karawar da Sporting ta doke Vitoria 3-0 a karshen mako, yayin da kungiyar ta Anfield ke neman sabon mai kai hari da kuma babban dan baya a bazaran nan. (HITC)

Matashin dan bayan Everton da tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Jarrad Branthwaite ya kasance na gaba-gaba da Manchester United ke son saye a bazaran nan, kuma United na son a yi cinikin da wuri. (Football Insider)

Real Betis na son daukar tsohon golan Manchester United da Sifaniya David de Gea, mai shekara 33, wanda tun lokacin da ya bar Old Trafford a karshen kakar bara ba shi da kungiya. (Estadio Deportivo)

Dan bayan Brazil Thiago Silva, mai shekara 39, zai bar Chelsea idan kwantiraginsa ya kare a bazaran nan. (Fabrizio Romano)

Crystal Palace na son dan wasan tsakiya na Leicester City Wilfred Ndidi, dan Najeriya mai shekara 27, wanda kwantiraginsa zai kare a bazaran nan. (Talksport)

Bayern Munich ta zuba ido ta ga yadda za ta kare a kanFrenkie de Jong na Barcelona, kodayake maganar albashin dan wasan na tsakiya na Holland mai shekara 26 ka iya hana cinikin.

People are also reading