Home Back

Bukatar sakar wa 'yan siyasa mara a Nijar

dw.com 3 days ago
Nijar | Sojoji | Juyin Mulki | Janar Abdourahamane Tchiani | Mohamed Bazoum
Jagoran gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tchiani

Ana dai samun mabambanta ra'ayoyi a kan batun sakar wa 'yan siyasa marar ta yadda za su gudanar da harkokin jam'iyyu a kasar, inda da dama ke ganin bukatar hakan na da nasaba da kalubalen da kasar ke fuskanta yayin da wasu ke ganin lokaci bai yi ba la'akari da kalubalen rikice-ikicen da ita kanta siyasar ke tattare da su. Jim kadan bayan juyin mulkin ne dai, sojojin da suka karbi ikon suka fitar da sanarwar soke kundin tsarin milkin kasar da kuma dakatar da duk wasu ayyukan siyasa a kasar. Bazo Ma'azou wani matashin dan siyasa ne kuma yana daga cikin masu ganin akwai bukatar cire takunkumin, la'akari da kalubalen da kasar ke fuskanta a fannin tsaro.

To saidai ga Mahamadou Ibrahim Tullu lokaci bai yi ba,  ganin yadda 'yan siyasa ke watsi da manufofin al'ummarsu. Hatta wasu 'yan siyasa ma, kamar Alhaji Jaffar Dubai na ganin barnar da 'yan siyasar suka yi ce ta janyo yanayin da kasar ta fada na juyin milkin. To sai dai ga Habibou Mai Gujiya duk da cewar akwai bukatar sojojin su tsaya su adaidaita al'amura, amman kuma za su iya amfani da kwarewar wasu daga cikinsu wajan gudanar da ayyukan ci-gaba a kasar. Wannan dai ba shi ne karo na farko da 'yan siyasar ke kiraye-kiraye ga junansu ba, kan su zo su hada karfi da karfe domin tunkarar kalubalen tsaro. Ko a lokacin Shugaba Issoufou Mahamadou da ma Mohamed Bazoum din ma, jam'iyyun siyasar kasar da dama sun yi mubaya'a ga masu mulkin domin cimma wannan manufa.

People are also reading