“Zargin Gobara”: Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji 243 Ya Yi Saukar Gaggawa a Legas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Jirgin Air Peace da ya taso daga Fatakwal ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Alhamis.
Wannan na zuwa kwanaki kadan bayan da jirgin Dana Air ya kwace yayin da ya sauka a tashar jirgin ta Legas, wanda ya jawo aka dakatar da ayyukansa.
Kamar yadda kamfanin jiragen Air Peace ya sanar a shafinsa na Twitter, lamarin ya faru ne bayan matukin jirgin ya ga alamar tashin gobara a wutsiyar jirgin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
"Muna so mu sanar da jama'a cewa mun gamu da wata tangarda a jirgin mu da ya tashi daga Fatakwal zuwa Legas a ranar 25 ga watan Afrilu, 2024.
"Yan mintuna kafin jirgin ya sauka, matukinmu ya lura da alamar tashin gobara a wutsiyar jirgin. Matukin ya dauki dukkanin matakan kariya tare da magance matsalar."
Sanarwar kamfanin ta nuna cewa tangardar na'ura ne kawai aka samu amma babu wata gobara da ta tashi a wutsiyar jirgin.
"Matukin jirgin ya yi gaggawar sanar da cibiyar kula da tafiye-tafiyen jiragenmu da ke Legas halin da ake ciki misalin karfe 5:37 na yamma."
- A cewar sanarwar.
Jirgin mai dauke da fasinjoji 243 da ma'aikata 12 an ce ya sauka lafiya a kan titin 18L na filin jirgin saman Legas, rahoton Channels TV.
A jiya Alhamis, 25 ga watan Afrilu, Legit Hausa ta ruwaito cewa gobara ta tashi a wani bangare na filin jiragen saman Murtala Muhammad da ke Legas.
An tattaro cewa hukumar gudanarwar filin jirgin ta dakatar da ayyukanin dukkanin jiragen sama a bangaren yayin da hukumar kashe gobara ta kai dauki.
Asali: Legit.ng