Home Back

‘Yan sanda sun kama wani mai shago da ya sace ‘yar makwabta ya turbudata cikin Firiji ya kulle

premiumtimesng.com 2024/5/18
‘Yan sanda sun kama wani mai shago da ya sace ‘yar makwabta ya turbudata cikin Firiji ya kulle

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wani da ake zargi da sace wata yarinya ‘yar shekara 10 tare da boye ta a cikin firiji.

Mai magana da yawun rundunar, Mansir Hassan, ya tabbatar da kama wanda ake zargin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Talata a Kaduna.

Hassan ya ce a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe biyu na rana, mahaifiyar yarinyar da aka sace, Uwaila Idris da ke kauyen Unguwar Gara a karamar hukumar Kauru ta jihar, ta kai rahoton bacewar diyarta ofishin ‘Yan sanda.

“Ta zo ofishin ‘yan sanda ne ta ba da rahoton cewa a ranar 26 ga Afrilu, da misalin karfe daya na rana, wani Aminu Garba ya sace ‘yarta ‘yar shekara 10 mai suna Hanifa Garba a cikin shagonsa.

Hassan ya ce da aka tambayi wanda ake zargin game da inda Hanifa take, ya musanta cewa bai san inda take ba.

Daga nan sai ya koma shagonsa ya rufe bakinta da hijabinta sannan ya turbudata a cikin Firijin sa ya kuma saka kwado ya kulle.

Matasan unguwa ne suka ce lallai sai an binciki shagon sa kaf kafin a yarda cewa ba shi ya sace yarinyar ba kamar yadda ya ke ta cewa, Da aka balle firijin sai aka ga Hanifa ciki kwance.

Zuwa yanzu dai an cafke she yana tsare wajen ‘Yan sanda a na ci gaba da bincike.

People are also reading