Home Back

Hukumar EFCC Ta Ayyana Tsohon Gwamna Matsayin Wanda Take Nema Ruwa a Jallo

legit.ng 2024/5/2

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

Hukumar na neman Yahaya Bello ne bisa laifukan da suka shafi almindahanar maƙudan kuɗaɗe.

EFCC na neman Yahaya Bello
Hukumar EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo Hoto: EFCC, Alhaji Yahaya Bello Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis, 18 ga watan Afirilun 2024.

Sanarwar na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, bisa laifukan da suka shafi almundahanar kuɗi har N80.2bn."
"Duk wanda ke da bayanin inda yake ya kai rahoto cikin gaggawa ga hukumar ko kuma ofishin ƴan sanda mafi kusa."

Asali: Legit.ng

People are also reading