Home Back

An ga jinjirin watan Zul-Hijjah a Najeriya, ranar Lahadi 16 ga watan Yuni Babbar Sallah

dalafmkano.com 2024/7/6

Fadar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar Sa’ad na uku, ta sanar da ganin jinjirin watan Zul-Hijjah na shekarar 1445.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da fadar Sarkin Musulmin ta fitar, mai ɗauke da sa hannun Wazirin Sakkwato, kuma shugaban kwamitin duban wata Farfesa Sambo Wali Junaid.

Sanarwar ta kuma ce duba da ganin jaririn watan na Zul-Hijjah da akayi a jiya Alhamis, hakan ya tabbatar da cewar yau Juma’a ɗaya ga watan Zul-Hijjah, wanda za’ayi babbar Sallah a ranar Lahadi 16 ga watan Yunin 2024.

Tun dai a jiya Alhamis hukumomi a ƙasar Saudiyya suka sanar da ganin Jaririn watan na Zul-Hijjah, lamarin da ya kasance za’ayi tsayuwar Arafa a ranar Asabar 15 ga watan Yunin 2024, yayin da za’ayi babbar Sallah a ranar Lahadi 16 ga watan na Yuni.

Kafar Dala FM Kano, ta rawaito cewa, kawo yanzu dai maniyyata aikin hajjin bana da dama ne ke ci gaba da shiga ƙasa mai tsarki, a ƙoƙarin su na zuwa domin sauke Farali.

People are also reading