Home Back

Kaduna: Martani kan binciken El-Rufa'i

dw.com 2024/7/15
Nigeria, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai
Hoto: picture alliance/AA/Stringer

Majalisar dokokin jihar Kaduna bayan kammala binciken da ya dauki watanni karkashin wani kwamitin da aka kafa, ta shawarci sabon gwanan jihar sanata Uba Sani da ya kaddamar da bincike dalla dalla kan tsohon gwamnan na Kaduna mallam Nasiri El-Rufa'i domin ya yi bayanin yadda ya kashe miliyoyin dalolin da ya ciyowa jihar yayin da yake jan ragamin shugabancin jihar

Da yake  karanta sakamakon binciken a harabar majalisar ,shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna Honorable Yusuf Dahiru Imam ya bayyana cewa sama da Naira biyalin 400 ne tshohuwar gwamnatin El-Rufa'i da makararrabansa suka yi awon gaba da su

Yace daga shekara da 2015 zuwa 2023 makudade kudade ne sama da biliyan 400 suka salwanta, a saboda da haka muke so  hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta binciki dukkanin wadanda suka cinye kudaden jihar.

People are also reading