Home Back

Gidauniyar kafa kamfanin magunguna a Afirka

dw.com 2024/7/5
Wasu shugabannin Afirka da na Turai
Wasu shugabannin Afirka da na Turai

Samar da kamfanin harhada magunguna a Afirka zai kasance matakin farko mai muhimmanci wajen samar da magani na hakika ga Afirka da kuma kasuwar maganin a nahiyar a cewar shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin jawabinsa wajen bude taron a birnin Paris.

Macron ya ce kashi uku cikin kashi hudu na kudaden za su fito ne daga tarayyar Turai.

Taron gidauniyar ya sami halartar shugabannin Botswana da Rwanda da Senegal da Ghana da ministocin lafiya da kuma kamfanonin harhahada magunguna.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz wanda ya gabatar da jawabinsa ta bidiyo ya ce Jamus za ta bayar da gudunmawar dala miliyan 318. Faransa ta bayar da dala miliyan 100, Burtaniya dala miliyan 60.

Sauran kasashen da suka bayar da gudunmawa sun hada da Amurka da Kanada da Norway da Japan da kuma gidauniyar Bil Gates.

Shugaban kungiyar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya ce shirin zai taimaka wajen samar da cigaban kamfanonin magunguna a Afirka da kuma hada hannu a tsakanin kasashe domin aiki tare.

People are also reading