Home Back

Gwamnati Ta Dauki Matakin Inganta Lafiyar Almajirai, Za Su Shiga Inshora a Gombe

legit.ng 2024/7/6
  • A kokarin gwamnatin jihar Gombe na kawo tsare-tsaren zamani a harkar karatun tsangaya da almajiranci ta dauki mataki kan kiwon lafiya
  • Gwamantin ta bayyana cewa akwai tsare-tsaren bayar da tallafi na kiwon lafiya da za ta kawo ga yara wanda almajirai za su ci gajiyar shirin
  • Dakta Abubakar Musa ne ya bayyana haka yayin ganawa da mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin karatun tsangaya da almajiranci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Gwamnatin jihar Gombe ta kara kawo shirin kiwon lafiya wanda almajirai da masu karatun tsangaya za su mora.

Shirin na daya daga cikin kokarin da gwamnan jihar Gombe ya ke na ganin ya zamanantar da almajiranci.

Gwamna Inuwa Yahaya
Za a ba almajirai tallafin lafiya a Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan ne a cikin wani sako da mai taimakawa gwamnatin Gombe kan harkokin sadarwa, Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gombe: Tallafin lafiya ga almajirai

Shugaban cibiyar lafiya ta GoHealth, Dakta Abubakar Musa ya bayyana cewa suna da shiri na tallafawa marasa karfi a kan harkar lafiya.

Dakta Abubakar Musa ya ce a karkashin tallafin za a saka almajirai da sauran masu karatun tsangaya domin ba su kulawa ta musamman.

Almajiran da za a ba tallafin lafiya

Shugaban cibiyar GoHealth ya ce ba za su iya bada tallafin ga dukkan almajiran da suke jihar Gombe ba a karon farko.

Sai dai ya tabbatar da cewa za su shigar da almajirai da suke karkashin makarantun zamani da gwamnatin jihar ke ginawa.

Tallafin lafiya ga almajirai zai taimaka

Mai ba gwamnan jihar Gombe shawara kan harkokin karantun tsangaya da almajiranci ta ce shirin zai yi matuƙar taimako ga almajirai.

Sayyada Aminatu Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta ce ya kamata wannan tsarin ta zamo abin koyi ga sauran jihohin Najeriya.

Za a gina makarantun allo a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya, ta Gombe da bankin raya Muslunci sun hada kai domin gina makarantun Almajirai a Gombe.

Rahotanni sun nuna cewa za a fara koyawa Almajirai Turanci da Larabci domin su zama 'yan kasa na gari kuma su daina yawo sakaka.

Asali: Legit.ng

People are also reading